Ku Daina Karba Idan Bankuna Suka Baku Tsoffi Naira, CBN Ya Umarci ’Yan Najeriya
- CBN ya zo da sabon salo, ya ce kada ‘yan Najeriya su ci gaba da karbar tsoffin Naira a halin da ake ciki na kusantar wa’adi
- CBN ya ce duk bankin da ya ba dan Najeriya tsohon kudi, to kada a karba, a kai korafi zuwa ga babban bankin
- Tun farko an umarci bankuna da su daina ba da tsoffin kudade a kan na’urorin ATM a kasar nan, amma ana samun masu bayarwa
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bukaci ‘yan Najeriya da su tubure game da karbar tsoffin kudade daga bankunan kasar nan, RFI ta ruwaito.
CBN ya ce wannan mataki ya zama dole domin kuwa wa’adin da ya debar kowa ya mayar da tsoffin kudin banki ya kusa zuwa karshe.
Idan baku manta ba, CBN ya ce za a daina amfani da tsoffin kudaden N200, N500 da N1,000 daga ranar 31 ga watan Janairun bana bayan buga sabbi.
Da take magana yayin wayar da kan jama’a game da sabbin kudaden kasar da kuma mayar da tsoffi banki a birnin Lokoja, Mataimakiyar Daraktan Sarrafa kudaden Bankin, Dr. Rekiyat Yusuf ta ce akwai bukatar mutane su dauki mataki
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A bangare guda, ta ce CBN ya tanadi hanyoyi masu tsauri don ladabtar da bakunan kasuwancin da ke ci gaba da ba da tsoffi kudade.
Ku kai korafi kan duk bankin da ke ba da tsohon kudi
Game da matakin da mutane za su dauka, CBN ya ce ‘yan kasa za su iya kai korafin bankin da suka gani yana ba da tsoffin kudade a kan na’urar ATM.
A cewarta, babu wani dalili da zai sa bankuna su ke ci gaba da ba da tsoffin kudade a daidai lokacin da suke da’awar daina karbarsu daga kwastomomin.
Daraktar ta kuma yi karin haske da cewa, an dauko kudurin sauya wasu daga kudaden Najeriya ne domin dakile aukuwar ayyukan ta’addanci da cin hanci da rashawa a kasar.
Hakazalika, ta ce sauyin kudin zai farfado da tattalin arziki tare da rage hauhawar farashin kayayyaki da ake gani a yanzu.
Wani rahoton The Guardian ya ce, har yanzu bankunan na ci gaba da ba da tsoffin kudade ga 'yan Najeriya.
CBN ya ce akwai sabbin kudade a kasa, bankuna sun ki zuwa su dauka har yanzu, amma za ta dauki mataki.
Asali: Legit.ng