Mutum 25 Sun Mutu A Yayin Da Sabuwar Mugunyar Cuta Ta Bulla A Kano

Mutum 25 Sun Mutu A Yayin Da Sabuwar Mugunyar Cuta Ta Bulla A Kano

  • A kalla mutane 25 sun riga mu gidan gaskiya a Kano sakamakon kamuwa da cutar diptheria
  • Dr Abdullahi Kauran-mata, kwararren likita a bangaren cututtuka masu yaduwa ya tabbatar kuma kwamishinan lafiya na Kano, Dr Aminu Tsanyawa ta ce a kalla mutum 25 sun rasu
  • Tsanyawa ya ce an kafa cibiyar kula da wadanda suka kamu a asibitin kwararru ta Murtala, ya kuma yi kira ga al'umma su kiyaye tsafta

Kano - A kalla mutane 15 ne suka rasu sakamakon abin da ake zargi cutar diptheria ne a jihar Kano zuwa ranar 18 ga watan Janairu, a cewar Dr Abdullahi Kauran-Mata, masanin cututtuka masu yaduwa.

Ya ce an samu mutum 78 masu dauke da cutar mai gaggawar yaduwa a kananan hukumomi 14 na jihar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Rayuka 2 na Matasan da Suka je Gyara Sokaway a Kano Sun Salwanta Bayan Sun Kasa Fitowa

Diptheria
Wata Sabuwar Mugunyar Cuta Ta Kashe Mutane 15 A Jihar Kano. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kauran-Mata ya fada wa kamfanin dillancin labarai NAN, a ranar Alhamis a Abuja, cewa an dauki samfuri guda 27 an kai su dakin gwaji, an tabbatar da takwas kuma mutane uku sun mutu a jihar.

Ya ce:

"A halin yanzu gwamnatin jiha ta kafa cibiyar kula da masu diphtheria da tallafi daga kungiyoyin tallafawa al'umma na Médecins Sans Frontières (MSF) a asibitin kwararru na Murtala Muhammad inda ake kula da masu dauke da cutar.
"An kuma fara sanarwa a gidajen radio tare da tattaunawa kan cutar.
"Gwamnatin jihar ta kuma kafa tawaga mai kula da yaduwar cutar karkashin jagorancin jami'in kula da bullar annoba don saka ido."

Akwai rigakafin cutar diphtheria

Kauran-mata ya ce ana iya kare kamuwa da diptheria ta hanyar rigakafi.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yankewa Matashi Hukuncin Kisa Kan Satar N57,000 a Jihar Legas

"Amma, kananan yara ake yi wa rigakafin karkashin tsarin riga kafi na kasa.
"Sauran hanyoyin kare kai daga kamuwa sun hada da saka takunkumin fuska, wanke hannu da tsafta, takaita taba wadanda suka kamu da kai su asibiti cikin gaggawa."

Gwamnatin Kano ta tabbatar da bullar cutar diptheria, ta ce mutum 25 sun rasu

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Tsanyawa ya tabbatar da bullar cutar inda ya ce akalla mutum 25 sun mutu, rahoton The Punch.

Kwamishinan wanda ya tabbata da bular cutar a ranar Alhamis ya ce jihar a shirye ta ke don daukan matakan magance cutar, yana mai cewaan kafa cibiyar magani kuma ana sa ido.

Alamomin cutar sun hada da ciwon makogoro, tari, zubar da yawu, sauyawan murya, kumburin wuya, wuyar numfashi, zazzabi ko warin baki da sauransu.

Legit.ng ta samu ji ta bakin wata baiwar Allah wacce cutar ta Diptheria (mashako) ta halaka yar ta a Kano.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Bindige Kansila Har Lahira A Jihar Arewa

Matar da ta nemi a sakaya sunanta, mai zaune a unguwar Kumbotso a Kano ta ce shekarun yarta biyu da rabi.

Ta cigaba da cewa ta yi zaton zazzabi ne da yara suka saba yi.

Kalamanta:

"Zazzabi ta fara sai ta kuma dena cin abinci. Da yake an yaye ta na yi zaton zazzabin cizon sauro ne, sai na rika bata maganin maleriya (zazzabin cizon sauro.
"Bayan kwana biyu sai na lura akwai wani farin abu daga karshen makogoro har zuwa bakinta. Daga nan ne na gane lallai ba lafiya sosai.
"Na jira washegari in kai ta asibiti amma jikin dare ta rasu."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164