Sojoji Sun Fatattaki ’Yan Bindiga, Sun Sheke 2 a Karamar Hukumar Chikun
- Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar hallaka 'yan bindiga biyu a yankin Chikun na jihar Kaduna a Arewa maso Yammacin Najeriya
- Wannan na zuwa ne daga bakin kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya bayyana martanin gwamnatin jihar
- An yi kaca-kaca da maboyar 'yan bindiga, an kuma kwato kayayyakin aikata laifuka daga hannun tsagerun
Chikun, jihar Kaduna - Dakarun rundunar Operation Forest Sanity sun hallaka wasu ‘yan bindiga biyu tare da kakkabe maboyar tsageru a yankin Chikun na jihar Kaduna.
Wannan batu na fitowa ne daga kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, inda yace jami’an sun yi nasarar wannan aikin ne a wani sintiri da suka yi a tsakanin Kaboresha-Dajin Rijana-Kuzo-Kujeni-Gwanto-Kachia.
Ya bayyana cewa, jami’an sun yi kwanton bauna ne a titin Gwanto-Kwasau, inda suka yi arba da ‘yan bindigan da ke tahowa a kan babura.
Ya ce jami’an sun hallaka ‘yan bindiga biyu nan take tare da kwato babura guda uku daga hannun tsagerun, kafar labarai ta Zagazola Makama ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An yi kaca-kaca da maboyar 'yan bindiga
A wani aikin na daba, dakarun tsaron sun yi kaca-kaca da sansanonin ‘yan bindiha a yankin Kutura-Rijana.
‘Yan bindigan sun tsere cikin daji yayin da suka ga jami’an tsaro, inda nan take aka lalata komai da ke cikin sansanin ‘yan ta’addan.
Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da kakin soja da sauran kayayyakin jami’an tsaro, PR Nigeria ta ruwaito.
Da yake yaba aikin sojoji, Aruwan ya ce gwamnati na ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumonin tsaro don tabbatar da tsaro.
Hakazalika, ya ce gwamnan jihar Kaduna ya ji dadin labarin lallasa ‘yan ta’addan kuma ya karfafa jami’an gwiwa tare da yaba musu bisa wannan namijin aikin.
An kama kakin soja jihar Legas
A bangare guda, rundunar Kwastam ta Najeriya ta kama wasu kayayyakin da aka shigo dasu Najeriya daga kasashen waje.
An kama kakin soha da na 'yan sanda a jihar Legas, an kawo su daga kasar Afrika ta Kudu, inji rahoto.
Hakazalika, an kama kwayoyin aji garau d aka shigo da su daga kasashen Paskistan da Indiya.
Asali: Legit.ng