Ya Yi Masa Kyau: Saurayi Dan Kankamo Ya Yi Kuskuren Turawa Budurwarsa N20k Sau Biyu, Ransa Na Kuna
- Wata matashiya yar Najeriya ta bayyana hirar ban dariya da ya gudana tsakaninta da saurayinta dan kankamo wanda ya yi kuskuren tura kudi asusun bankinta sau biyu
- Saboda matsalar network saurayin nata ya tura mata N20,000 sau biyu bisa rashin sani sannan ya roke ta a kan ta mayar masa da shi
- Sai dai kuma ta ki mayar masa da kudin cewa bata da isasshen kudin aika kudin a asusunta
Wata matashiyar budurwa yar Najeriya, Boujee Jessie, ta bayyana yadda saurayinta dan kankamo ya tura N20k sau biyu zuwa asusunta bisa kuskure.
Saurayin nata ya tura N20,000 sau biyu zuwa asusun bankinta saboda matsalar ‘network’.
Da ya gano cewa ya tura kudin sau biyu, nan take sai ya aika mata sako ya WhatsApp, yana neman ta dawo masa da N20k.
Sai dai kuma, budurwar ta ki. Maimakon haka, ta fada ma saurayin nata cewa bata da kudin mayar masa da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Saurayin nata ya roke ta cewa idan ta tura masa N20,000 din, zai tura mata na cajin banki.
Daga bisani ta fallasa hirar tasu a soshiyal midiya dauke da taken:
“A yayin da saurayinka dan kankamo ya tura maka kudi sau biyu bisa kuskure.”
Ta kuma nemi shawarar mutane kan ko ta mayar masa da kudin ko ta fuske.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
@Victor funds ya rubuta:
“Ki mayar masa da kudin don kada ya zabtare sadakinki.”
@bigmax196 ya ce:
“Lol kankamo sannan ya baki kudi me yasa baki tura masa ba.”
@Gabby ya yi martani:
“Ba dai har kin ci na kare ba.”
@Timeyin D. ta ce:
“Zan ce sau biyu a ina??? Ban ga kowa ba. Ka gwada sake turawa.”
Budurwa mai karban albashi rabin miliyan na neman mijin aure
A wani labarin kuma, mun ji cewa wata budurwa yar asalin jihar Adamawa da ke zaune a Abuja ta ce tana neman mijin aure.
Budurwar ta baza neman miji a dandalin kulla soyayya ta Musulunci inda ta ce tana son namiji mai hankali da aiki mai kyau.
Ta kuma bayyana cewa tana karban rabin miliyan duk wata a matsayin albashinta.
Asali: Legit.ng