Tsohon Minista, Lauyoyi, Sun ja Kunne kan Amfani da DSS wajen cafke Gwamnan CBN

Tsohon Minista, Lauyoyi, Sun ja Kunne kan Amfani da DSS wajen cafke Gwamnan CBN

  • Wasu manyan Lauyoyi sun tsoma baki a kan sabanin Gwamnan CBN da jami’an tsaron Najeriya
  • Ana zargin Hukumar DSS da kokarin cafke Godwin Emefiele duk da kotu ta haramta mata yin hakan
  • Lauyoyi sun nemi alfarma wajen AGF, sun ce Abubakar Malami SAN ya ja-kunnen Hukumomi

Abuja - Manyan Lauyoyi hudu da sun kai matsayin SANs da tsohon Ministan shari’a sun yi tir da yunkurin cafke Gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Leadership ta fitar da rahoto a farkon makon nan cewa masana shari’ar sun soki kokarin da ake yi na kama Godwin Emefiele bisa zargin ta’addanci.

Daga cikin wadanda suka sa hannu a wasikar da aka aikawa gwamnatin tarayya akwai tsohon Ministan shari’a na kasa da wasu lauyoyin tsarin mulki.

Adetokunbo Kayode, Oba Maduabuchi, Emeka Ozoani, M.M Nurudeen, Abdul Mohammed, da Dr. Emeka Obegolu sun ce sun ga take-taken jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Babban Banki Ya Koma Bakin Aiki, CBN Ya Fitar da Sabuwar Sanarwa

Za a ketawa Gwamnan CBN alfarma

Lauyoyin sun ce ana kokarin yin watsi da umarnin da kotu suka yi, ayi ram da Gwamnan babban bankin wanda hakan danne masa hakki ne a doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna a farkon watan Junairun 2023 ne Lauyoyin suka rubutawa Ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN) wasika a kan batun Emefiele.

Gwamnan CBN
Wasu Jami'an 'Yan Sandan Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A bar doka tayi aiki - Lauyoyi

Wadannan Lauyoyi sun bukaci babban lauyan na gwamnatin tarayya ya bar doka tayi aiki.

Abin da lauyoyin nan suka nema shi ne a matsayinsa na Ministan shari’an tarayya, Malami ya tabbatar gwamnati da jami’an tsaro ba su taka doka ba.

Wasikar ta ce duk da hukuncin da kotun tarayya suka yanke a kan bukatar DSS wajen tsare gwamnan CBN, an cigaba da kokarin a hana shi aikinsa.

Vanguard ta ce wannan ya sa aka nemi Malami SAN ya yi amfani da kujerarsa, ya ja-kunnen masu iko da su yi wa dokar kasa biyyaya, su bi umarnin kotu.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Yadda Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi Za Suyi Yaki a Kan Kuri’un Kano

Kayode, Maduabuchi, Ozoani, Nurudeen, Mohammed, da kuma Obegolu suka ce kotu ce gatar gwamnati da mara gata, don haka bai kamata a saba mata ba.

Tirka-tirkar Gwamnan CBN

Bayan shafe kwana da kwanki ba a san inda ya shiga ba, kwanaki aka ji labari cewa Gwamnan CBN watau Godwin Emefiele ya lallabo ya shigo Najeriya.

Da aka taso shi a gaba, Godwin Emefiele ya nemi hutu a wajen shugaban kasa, yanzu da hutunsa ya kare, dole ya dawo bakin aiki duk da barazanar DSS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng