Hauhawar Farashin Kayayyaki a Najeriya Ya Sauka Zuwa 21.34%, Karon Farko Cikin Watanni 11

Hauhawar Farashin Kayayyaki a Najeriya Ya Sauka Zuwa 21.34%, Karon Farko Cikin Watanni 11

  • Hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayyana yadda hauhawar farashin kayayyaki ya ragu a Najeriya
  • Hukumar ta ce a karon farko cikin watanni 11, an samu raguwar hauhawar farashi, ya sauka zuwa 21.34%
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan yadda farashin kayayyaki ke yi tashin gwauron zabi a shekarun nan

FCT, Abuja - Labarin da muke samu daga majiyar tattalin arziki a Najeriya ya bayyana cewa, hauhawar farashi a kasar ya sauka da 21.34% cikin watanni 11.

Wannan kididdiga ne mai zuwa daga CPI mai kula da farashin kayayyaki a Najeriya.

Wannan sauyi da aka samu ya zo ne karshen watan Disamban 2021, kuma shi ne karo na farko da kayayyaki suka sauya cikin watanni 11.

Hauhawar farashi ya ragu
Hauhawar Farashin Kayayyaki a Najeriya Ya Sauka Zuwa 21.34%, Karon Farko Cikin Watanni 11 | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar cikakken rahoto game da yadda hauhawar farashin kayayyaki ya sauka a kasar.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata, EFCC Ta Gama Shirin Kama Gwamnonin Jihohin da Za Su Bar Ofis

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

NBS ta ce, an samu ragin 0.13% a watan Disamban bara idan aka kwatanta da yadda farashin yake a watan Nuwamba.

Sassauci a farashin abinci a Najeriya

A bangaren kayan abinci, NBS ta ce an farashin ya sauka daga 24.13% zuwa 23.75% a watan na Disamban bara.

Amma a duba da kwatancen farashin na shekara-shekara, kason ya karo da 6/38% idan aka kwatanta da shekarar 2021 da ta gabata.

'Yan Najeriya na cu gaba da nuna damuwa game da yadda kayayaki ke kara farashi a kasar nan, musamman a shekarun bayan nan.

Nufin Allah: Abdul Samad ya zama na 4 cikin attajiran da suka fi kudi a Afrika

A wani labarin kuma, kun ji yadda attajiri dan Najeriya kuma Bakano ya zama na hudu a jerin masu kudi a nahiyar Afrika gaba daya.

Kara karanta wannan

Saura Watanni 2 Ya Bar Ofis, Buhari Ya Karfafi Muhimmin Aikin da Ya Tattago a Arewa

Idan baku manta ba, Aliko Dangote ne na farko a jerin masu kudin Aftika, yanzu Abdul Samad ya zama na daga cikin jerin su Dangote, kamar yaddda rahotanni suka bayyana a karshen shekarar da ta gabata.

Abdul Samad ne shugaban kamfanin samar kayayyakin amfanin yau da kullum na BUA, kuma kamfaninsa ke gogayya da na Dangote wajen siyar da filawa, sukari, siminti da sauran kayayyaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.