An Shiga Tashin Hankali a Bauchi Kan Filin da Za'a Maida Makabartar Kiristoci

An Shiga Tashin Hankali a Bauchi Kan Filin da Za'a Maida Makabartar Kiristoci

  • Mabiya addinin Musulunci a yankin Yolan Bayara da ke jahar Bauchi sun nuna adawarsu da shirin da gwamnati ke yi na bayar da fili ga al'ummar kirista
  • Gwamnatin Bala Mohammed dai ta mallakawa kiristoci a jihar fili mai fadin hekta 470 domin su mayar da shi makabatarsu a yankin na Yolan Bayara
  • Kakakin gwamnan jihar ya ce har yanzu ba a mika filin ga kiristoci ba a hukumance, inda ya bukaci al'ummar yankin su kwantar da hankalinsu

Bauchi - Al'ummar Musulmai a yankin Yolan Bayara da ke wajen garin Bauchi sun rubuta korafi a kan matakin da gwamnatin jihar Bauchi ta dauka na bai wa al'ummar Kirista fili domin su mayar da shi makabartar kirista.

Sun yi zanga-zanga a rubutacciyar karar mai kwanan wata 10 ga watan Janairu kuma an aike shi ga Gwamna Bala Mohammed ta hannun sakataren gwamnatin jahar.

Kara karanta wannan

2023: Bidiyon Yadda Aka Ceci Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Tulin Jama'a Ya Fito

Jahar Bauchi
An Shiga Tashin Hankali a Bauchi Kan Filin da Za'a Maida Makabartar Kiristoci Hoto: Leadership
Asali: UGC

Korafin na dauke da sa hannun Sani Sarki Yakubu da wasu mutum shida wanda aka mika kwafi ga dukkanin hukumomin tsaro a jihar, Sarkin Bauchi, Ciyaman Jamatu Nasiril Islam, Jahar Bauchi, Shugaban JIBIWIS, Jahar Bauchi.

An kuma bukaci gwamnan da ya dauki matakin gaggawa domin hana barkewar rikicin a tsakanin al'umma, Daily Trust ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga bisani Yakubu ya yi jawabi ga taron manema labarai a madadin al'ummar Musulmi a karshen mako a garin Bauchi.

Sun yi ikirarin cewa gaba daya filin mai fadin hekta 470 wanda a ciki ne za a bayar da hekta 50 don gina makabartar na al'ummar Musulmi ne, rahoton Punch.

Ba a riga an bai wa Kiristoci filin ba a hukumance, kakakin gwamnan Bauchi

Da yake martani ga korafin, kakakin gwamnan jihar Bauchi, Mukhtar Gidado, ya ce gwamnatin bata riga ta bayar da filin ga al'ummar Kirista ba a hukumance, yana mai cewa har yanzu gwamnati na nazari a kan tsare-tsare.

Kara karanta wannan

'Dan Takarar Gwamna a 2023 Ya Yi Alƙawarin Kafa Gwamnati Bisa Koyi da Annabi Muhammad SAW

Ya kuma bukaci al'ummar yankin da su kwantar da hankalinsu, rahoton Punch.

Gwamna Bala Mohammed ya bai wa kiristoci fili mai fadin hekta 50, Shugaban CAN

Ku tuna cewa Shugaban CAN na Bauchi, Rev. Dr Abraham Demius Damina, ya sanar da cewar Gwamna Mohammed ya ba su fili mai fadi hekta 50 domin amfani da shi a matsayin sabuwar makabartarsu.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a gidan gwamnatin Bauchi.

Da yake martani, Gwamna Mohammed ya ce taron ya gudana ne don neman taimakon Kiristocin Bauchi wajen yi masa addu'a a yayin da yake neman kudirinsa na zarcewa kan kujerar mulki.

PDP ta yi babban kamu na mambobin APC a jihar Bauchi

A wani labari na daban, mambobin jam'iyyar APC fiye da 20,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Bauchi.

Masu sauya shekar sun ce sun dawo jam'iyyar adawa ne saboda nasarorin da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel