Na Fice Daga APC Ne Domin Gujewa Shugabancin Yaudara, Inji Tsohuwar Shugabar Matan Jam'iyyar

Na Fice Daga APC Ne Domin Gujewa Shugabancin Yaudara, Inji Tsohuwar Shugabar Matan Jam'iyyar

  • Jam'iyyar APC ta samu martani mai zafi daga wata shugabar matanta, Beatrice Nkwuda game yiwuwar dawowarta jam'iyyar gabanin zabe
  • Beatrice Nkwuda a wata tattaunawa ta ce ba za ta sake dawowa APC ba saboda yanzu ta samu mafaka a jam'iyyar APGA mai zakara
  • Tsohuwar jigon a APC ta ce ta bar APC ne saboda halin kankamo da yaudara irin na gwamna Umahi na jihar Ebonyi

Beatrice Nkwuda, tsohuwar shugaban matan jam'iyyar APC a Ebonyi ta tsakiya ta magantu kan dalilin da yasa ta fice daga jam'iyyar ta koma wata daban.

Yayin wata tattaunawa ta musamman da New Telegraph, Nkwuda ta yi ikrarin cewa, ta fita daga jam'iyyar ne bayan da wasu 'yan mamayar PDP suka shigo ta ta dalilin gwamna Umahi a lokacin da ya dawo APC.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Kamfe Domin Ta Ya PDP Jimamin Abinda Ya Auku a Jihar Arewa

A cewarta, kafin shigowar Umahi APC, ita da abokanta a jam'iyyar na cikin zaman lafiya da 'yanci, amma komai ya sauya lokacin da ya ingiza kansa ga jam'iyyar.

Beatrice Nkwuda ta fadi dalilin barinta APC
Na Fice Daga APC Ne Domin Gujewa Shugabancin Yaudara, Inji Tsohuwar Shugabar Matan Jam'iyyar | Hoto: newtelegraphng.com
Asali: UGC

Gwamna Umahi ne sila

Ta kuma bayyana cewa, gwamnan na Ebonyi ya mamaye komai ba tare da la'akari da tsoffin jiga-jigan jam'iyyar ba, inda tace ya gaza damawa dasu a shugabancinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana cewa:

"Ban jin natsuwa game da mutanen da nake wakilta a matsayina na shugabar mata saboda hakan. Na barta. Dole yasa na bar jam'iyyar saboda dabi'ar yaudararsu; ba su da karamci.
"Haka nan abu mafi hmuhmmanci, ba sa ba kowa 'yan dan adamtaka wanda ke rubutr a kudin tsarin mulki."

Ba ni ba APC, inji Beatrice Nkwuda

Da aka tambaye ta me za ta ce idan ta samu dama aka ce ta dawo jam'iyyar APC gabanin zaben da ke tafe, ta shaidawa New Telegraph cewa:

Kara karanta wannan

Makonni Gabanin Babban Zabe, Babban Jigon APC Kuma Tsohon Kwamishina Ya Bar Tsagin Tinubu

"Allah ya sawwke! Ta yaya hakan zai faru a gwamnatin da kwana nawa ne ya rage mata? Na kasance a can, ba zan koma garesu ba. Ta yaya zan koma wurinsu bayan kwanaki kadan ya rage su tafi?
"Gwamnatin har ta tantance ni cikin kwamitin kamfen dinta amma na ki na koma tsagin APGA."

A bangare guda, hukumar zabe a Najeriya dai na ci gaba da shirin zabe, ta gayyaci shugabannin jam'iyyun siyasa don sanar dasu halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.