Dan Takarar Shugaban Kasa a PDP, Atiku Ya Dawo Najeriya Bayan Shafe Kwanaki a Ingila
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya dawo Najeriya bayan shafe kwanaki a kasar Burtaniya
- Atiku ya je Landan ne domin tattaunawa da shugabanni a can kana ya kulla wata alaka da kasar gabanin zaben 2023
- An ruwaito a baya yadda kasar ta gayyace shi, ta ce tana son sake kulla alaka mai karfi da Najeriya bayan zaben 2023
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sauka a jirgi a Najeriya yayin da ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa kasar Burtaniya.
Tsohon hadimin shugaban kasa Jonathan, Reno Omokri ya yada bidiyon lokacin da Atiku a yau Juma'a 13 ga watan Janairun 2023.
A bidiyon, an ga Atiku tare da abokin takararsa, gwamna Okowa, gwamna Udon Emmanuel, gwamna Tambuwal, sanata Dino Melaye da tsohon shugaban PDP na kasa Uche Secondus.
Hakazalika, an ga tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidka da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a tare da Atiku.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meye ya kai Atiku kasar Burtaniya?
Jigon jam'iyyar PDP ya bayyana gaskiyar dalilin da yasa Atiku Abubakar ya shilla kasar waje ya kuma yu karin haske game da makomar siyasarsa.
Dele Momodu ya fito ya yi bayani, ya ce kasar Burtaniya ce ta gayyaci Atiku don tattauna matsayarsa kan harkallolin da za su kulla bayan ya lashe zabe a 2023.
Hakazalika, Dele Momode ya ce, akwai haske a bangaren Atiku, domin kuwa kasar ta Burtaniya ta fahimci tafarkin dan takarar da kuma abubuwan da yasa a gaba.
Duk da haka, Atiku na ci gaba da fuskantar barazana daga wasu gwamnonin PDP da sua ware suka ce sam basu gamsu da shugabancin jam'iyyar ba kwata-kwata.
Daya gwamnonin G-5 ya ce babu ruwansa da Atiku, ba kuma zai kakaba ma mutensa kowa ba
A bangare guda, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya ce sam bai da shirin goyon bayan Atiku saboda saba muradinsa a shugabancin PDP.
Ya kuma bayyana cewa, idan ya zabi dan takarar shugaban kasan da yake so, ba zai kakaba ma jama'ar jiharsa dole su bi shi ba.
Ortom na adawa da shugabancin PDP ne tare da wasu gwamnonin Kudancin Najeriya.
Asali: Legit.ng