Direban Tirela Tsere Bayan Kashe Jami'in NSCDC A Babban Jihar Arewa

Direban Tirela Tsere Bayan Kashe Jami'in NSCDC A Babban Jihar Arewa

  • Wani direban tirela ya yi ajalin jami'in hukumar tsaro ta NSCDC a garin Minna, babban birnin Jihar Neja
  • Jami'in na NSCDC ya tafi gida ne a kan babur dinsa kirar Jincheng yana dawowa domin yin aikin dare sai tirelan ta buge shi
  • Rahotanni sun bayyana cewa direban tirelan bai tsaya ba, ya fizgi motarsa ya tsere kuma da mutane suka taho taimakawa wanda abin ya faru da shi, bai dade ba ya karasa

Minna, Jihar Neja - Wata tirela a daren ranar Laraba ta kashe wani jami'in hukumar tsaro ta NSCDC a kasuwar zamani ta Kure a Minna, Jihar Neja, rahoton the Nation.

Marigayin, wanda ke aikin dare a ofis, ya tafi gida a kan babur dinsa kirara Jincheng kuma yana hanyar dawowa ofis ne tirelan ta buge shi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tsohon Daraktan Kamfen Shugaban Kasa Ya Magantu Bayan DSS Ta Cafke Shi a Filin Jirgi

Taswirar Neja
Direban Tirela Tsere Bayan Kashe Jami'in NSCDC A Babban Jihar Arewa. Hoto: The Nation.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Direban tirelen ya tsere, ya bar marigayin a hanya a yayin da mutane da ke wucewa suka yi kokarin taimaka masa suka kai shi amma ya mutu nan take.

Ba A Gano Lambar Tirelan Da Ta Halaka Jami'in NSCDC Ba, FRSC

Kwamandan hukumar kiyayye haddura na kasa, FRSC, na jihar Neja, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce hatsarin ta yi sanadin rasuwar direban tirelan amma ba a san inda ya nufa ba sannan ba a san lambar da ke jikin tirelan ba.

Ya ce jami'an NSCDC sun mika wa iyalan mammacin gawarsa a nan take bayan afkuwar hatsarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164