Hukumar Zabe INEC Ta Kara Wa'adin Karban Katin PVC Zuwa Karshen Wata

Hukumar Zabe INEC Ta Kara Wa'adin Karban Katin PVC Zuwa Karshen Wata

  • Ana saura kwanaki goma, hukumar INEC ta karawa yan Najeriya kwanaki takwas don karban katunan PVC
  • INEC ta zabe yan Najeriya sama da milyan 93 suka yi rijistan zabe kuma ake sa ran zasu kada kuri'a
  • Katin PVC ake amfani da shi wajen tantance duk mai niyyar ka'da kuri'a kafin a bari ya yi

Abuja - Hukumar shirya zaben kasa watau INEC ta kara wa'adin karban katunan zabe na PVC saboda yan Najeriya su samu damar musharaka a zaben 2023.

Hukumar ta sanar da hakan a jawabin da kwamishanan yada labaranta, Festus Okoye, ya fitar, rahoton ChannelsTV.

Da farko INEC ta ce ranar 22 ga Junairu, 2023 za'a rufe karban katunan zabe.

Amma yanzu hukumar bayan zamanta na ranar Alhamis ta dage ranar da kwanaki takwas.

Kara karanta wannan

An Tono Babban Abinda APC Ta Rasa a Arewa Wanda Zai Ja Wa Tinubu Shan Kaye a Zaben 2023

A cewar jawabin:

"Hukumar na son tabbatar da cewa dukkan mutanen da suka yi rijista sun samu damar karban katinsu na PVC gabanin zabe mai zuwa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Saboda haka, an kara wa'adin karban PVC da kwanaki takwas."
"Maimakon rufe karba ranar Lahadi, 22 ga Junairu 2023, za'a cigaba da karban katin zuwa ranar 29 ga Junairu 2023. A yanzu, ana karban katin daga karfe 9 na safe zuwa 3 na ranar (har da Asabar da Lahadi)."

INEC Chair
Hukumar Zabe INEC Ta Kara Wa'adin Karban Katin PVC Zuwa Karshen Wata
Asali: Original

Ya yi bayanin cewa an samu canji kan yadda yan Najeriya zasu iya karban katunan, yace:

1. An kara wa'adin karban katuna da gundumomi da mako guda daga Litinin 16 zuwa Lahadi 22 ga Junairy, 2023.

2. Za'a koma karba a kananan hukumomi daga ranar Litinin 23 zuwa Lahadi 29 ga Junairu 2023.

A cewarsa, an samu rahotannin wasu jami'an INEC na karban kudi hannun mutane a cibiyoyin karban katin kuma sun kaddamar da bincike kan hakan, riwayar Vanguard.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: IGP ya Samu Takardar Umarnin Kamo ‘Dan Takarar Gwamnan Akwa Ibom Kan Zargin Damfara

Yace:

"Duk wanda aka kama zai fuskanci ladabtarwa ko kuma a gurfanar da shi."
"An umurco kwamishanonin jihar RECs da su tabbatar da cewa irin haka bai faruwa a fadin tarayya kuma su dau matakin gaggawa."

Hukumar Zabe ta INEC ta Bayyana Yawan 'Yan Najeriya da Zasu Kada Kuri'a a Zaben 2023

INEC ta fitar da adadin yan Najeriya da sukayi rijista kuma ake sa ran zasu yi musharaka a zaben 2023.

INEC tace ta ce mutum 93,469,008 sukayi rijista domin zaben 2023 mai gabatowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida