Buhari Ya Bayyana Ainihin Manufar Ƙirƙirar Ƙungiyar Boko Haram
- Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce Boko Haram mummunar akida ce da aka kirkira don lalata Najeriya
- Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 11 ga watan Janairu yayin da kungiyar bishop-bishop na kungiyar katolika suka kai masa ziyar a fadarsa a Abuja
- Shugaban kasar ya ce gwamnatinsa ta samu nasarori sosai a bangaren yaki da ta'addancin musamman a jihar Borno da sauran jihohin arewa maso gabas
FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Boko Haram wata yaudara da makirci da aka kirkira domin a lalata Najeriya, rahoton Daily Trust.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da ya tarbi mambobin kungiyar bishop-bishop na darikar katolika, CBCN, a gidan gwamnati a Abuja.
Ya soki akidar yan ta'addan wanda ya ce sun hana mutane samun ilimi wanda ke shafan cigaban ilimin al'ummar yankin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaba Buhari ya ce za a dora kan cigaban da ya samu a bangaren tsaro, sannan za a mayar da hankali kan tattalin arziki kafin mika mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Buhari ya ce an samu cigaba a bangaren tsaro cikin yan shekarun nan musamman a arewa maso gabas musamman a bangaren gine-gine da ilimi.
Ya ce:
"Na gode bisa ziyarar da kuka kawo fadar shugaban kasa, na yarda da wasu abubuwan da kuka fada. Maganar tsaro na da muhimmanci gare mu don idan ba zaman lafiya, ba za a iya tafiyar da kasa ba.
"Ban dade da dawowa daga jihohin Adamawa da Yobe ba, Yayin ziyarar jihohin, na saurari abin da mutane da jami'ai suka ce. Duk sun ce an samu cigaba daga 2015 musamman jihar Borno.
"Boko Haram wata yaudara da makirci da aka kirkira domin a lalata Najeriya. Ba za ka iya cewa kada mutane su yi ilimi ba; akwai bukatar mutane su bunkasa ta hanyar ilimi."
Buhari ya ce bayar da nagartaccen ilimi ne zai kawo karshen Boko Haram
A bangare guda, Shugaban an Najeriya ya bukaci iyaye da masu kula da yara su tabbatar sun tura yaransu makaranta don su samu ilimi mai amfani tare da kawar da tunanin Boko Haram.
Shugaban ya roki yan jihar Yobe su zabi jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben da ke tafe daga sama har kasa, Punch ta rahoto.
Mr Femi Adesina, kakakin Shugaba Buhari ya ce shugaban kasar ya furta wannan jawabin ne wurin taron kamfen din dan takarar shugaban kasa da gwamna a jihar Yobe.
Asali: Legit.ng