Dalilin da Ya Sa Gwamnatin Burtaniya Ta Gayyaci Atiku, Majalisar Kamfen Dinsa Ta Magantu
- Atiku Abubakar ya samu gayyata daga gwamnatin Burtaniya, an tattauna dashi kan wasu batutuwa
- Jam'iyyar PDP ta fito ta yi bayani, ta bayyana gaskiyar abin da dan takarar na PDP ya tattauna da Burtaniya
- Hakazalika, PDP ta ce akwai haske ga Atiku a zaben shugaban kasa da za a yi nan da wata guda a Najeriya
Najeriya - Majalisar kamfen din takarar shugaban kasa ta jam'iyyar PDP ta bayyana dalilin da yasa gwamnatin kasar Burtaniya ta gayyaci Atiku don tattaunawa dashi, New Telegraph ta ruwaito.
A cewar majalisar, an gayyaci Atiku ne domin tattauna batutuwan da suka shafi gamayya da hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Burtaniya a nan gaba idan ya gaji Buhari.
Wannan na fitowa ne daga daraktan yada labaran majalisar, Otunba Dele Momodu a cikin wani sako da ya bayar a jiya Talata 10 ga watan Janairu.
Akwai yiwuwar Atiku ya lashe zabe, inji Dele Momodu
Momodu ya kuma bayyana cewa, akwai haske mai kyau game da nasarar Atiku a zaben da za a gudanar a cikin watan Fabrairu mai zuwa, rahoton Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar sakon nasa:
"Majiya ciki ta naqalto cewa, zaben ciki gida a na gwamnatin Burtaniya ya nuna AA (Atiku Abubakar) ne dan takarar da kan gaba kuma akwai yiwuwar aiki kafada-kafada dashi don amfanin kasashen biyu.
"Wannan na da matukar muhimmanci domin Burtaniya na son habakawa da fadada alakar kasuwanci da Najeriya."
Rikicin da ke gaban Atiku a matakin jam'iyya
Duk da wannan, har yanzu dan takarar na shugaban kasa a PDP na ci gaba da fuskantar barazana da koma baya a jam'iyyar, kasancewar akwai wasu jiga-jigan jam'iyyar da ke adawa dashi.
Gamayyar gwamnonin G-5 na ci gaba da nuna adawa da shugabancin PDP a matakin kasa, kana sun ce babu ruwansu da Atiku.
Gwamnonin dai burinsu shine; su ga an tsige Ayu Iyorchia ammatsayin shugaban jam'iyyar na kasa tare da ba wani dan yankin Kudu.
Burtaniya ba za ta tsoma baki a zaben bana ba
A tun farko kun ji cewa, kasar Burtaniya ta ce ba za ta sanya baki a zaben da za a gudanar a Najeriya ba kwata-kwata.
Wannan na fitowa ne daga bakin Ms Catriona Laing, babbar kwamishiniyar Burtaniya a Najeriya lokacin da take magana game da zaben na bana.
Ta kuma bayyana cewa, kasar ta Turai za ta tsaya ne tsaka-tsaki kan dukkan abubuwan da za su faru a zaben.
Asali: Legit.ng