An Samu Cig Gaba, Shugaba Buhari Zai Kaddamar da Jirgin Saman da Aka Kera a Najeriya

An Samu Cig Gaba, Shugaba Buhari Zai Kaddamar da Jirgin Saman da Aka Kera a Najeriya

  • Rahoton da muke samu daga jihar Kaduna ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar jirgin sama kirar Najeriya
  • An kirkiri jirgin sama mai saukar ungulu wanda komai nasa a Najeriya aka samar, kuma an ce zai fara aikin nan kusa
  • A tun farko hukumomin Najeriya sun bayyana aiki tukuru da suka yi wajen samar da wannan babban aiki na jirgi

Jihar Kaduna - Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya zai kaddamar da wani jirgi mai saukar ungula da aka kera a Najeriya, inji hukumar samar da kayayyakin kimiyya ta Najeriya (NASENI).

Hukumar ta ce, Buhari zai kaddamar da wannan babban aikin ci gaba ne da aka yi a Najeriya kafin ya sauya a mulki a zaben 2023 da ke tafe nan da wata guda mai zuwa, rahoton Aminiya.

Kara karanta wannan

A Gaban Buhari a Yobe, Bola Tinubu Ya Faɗi Matakin da Zai Dauka Kan ASUU Idan Ya Ci Zaben 2023

Wannan batu na fitowa ne daga bakin shugaban hukumar Farfesa Mohammed Sani Haruna yayin da ya kai wata ziyara ga kwamandan makarantar fasaha ta rundunar soji (AFIT), AVM Paul Jemitola, a ranar Talata 10 ga watan Janairu.

An kirkiri jirgi a Najeriya, Buhari zai kaddamar dashi
An Samu Cig Gaba, Shugaba Buhari Zai Kaddamar da Jirgin Saman da Aka Kera a Najeriya | Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoto ya bayyana cewa, Farfesa Mohammed ya kai ziyara ga babban jami'in sojin ne don tattauna batutuwa da ke alaka da yadda aikin jirgin mai sauakr ungula zai kasance.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An hada wasu jirage 2 a Najeriya, inji shugaban NASENI

Shugaban hukumar ta NASENI ya kuma bayyana cewa, tuni an yi nasarar kera jirage biyu a Najeriya, kuma a yanzu haka ana kan aikin kammala wani jirgin da komai nasa a Najeriya aka samar dashi.

A kalamansa:

“Idan komai ya tafi yadda ake so, shugaban kasa zai kaddamar duk abin da aka sami damar kammalawa kafin ya bar ofis ranar 29 ga watan Maris din 2023.”

Kara karanta wannan

Abin Duniya Bai Dameni Ba, Ku Rike Amana: Shugaba Buhari

Makarantar soji ta yi alkawarin kera jirgin da zai kafa tarihi a Najeriya

A wani alkawari da makarantar soji ta AFIT ta yi, ta ce za ta kera jirgin da zai kafa tarihi a Najeriya, kamar yadda kwamandan ya bayyana, The Guardian ta ruwaito.

Hakazalika, kwamandan ya bayyana jin dadinsa da yadda aka samu ci gaba mai kyau a Najeriya, musamman ta fannin jiragen sama

AFIT dai makaranta ce a karkashin rundunar sojin saman Najeriya, kuma tana aiki kafada-kafada a karkashin hukumar NASENI.

Idan baku manta ba, a baya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da jirgin ruwan da sojin ruwan Najeriya suka kera a nan gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.