Yadda Yan Nigeria Ke Ta'ammali Da Maganunuwan Da Zasu Illartar Dasu Basu Sani Ba

Yadda Yan Nigeria Ke Ta'ammali Da Maganunuwan Da Zasu Illartar Dasu Basu Sani Ba

  • Maganunuwa gargajiya sun zame wasu maganunuwa masu sauki da mutane ke ganin yafi saukin samu fiye da na bature kona zamani
  • Maganunuwa masu tallensu na ikirarin suna samun su ne daga itacuwa ko ciyayi a jeji ko a cikin gari
  • Abin mamakin shine yadda za'a tarar da maganin gargajiya guda daya amma yana maganin sanyi, ulsa, ciwon baya da wasu ciwuka da suke yawan damun mutane.

Nigeria - Hukumar kula da lafiya ta duniya WHO, tace kashi 80 cikin dari na kasashe masu tasowa sun dogara ga maganunuwan gargajiya, da kuma kananun cibiyoyin lafiya masu bayar da agajin gaggawa.

Wani bincike da wata jarida tayi a Nigeria ta gano dalilin da yasa Yan Nigeria ke ta'amali da maganin gargajiya duk da yadda suke da tarun matsaltsalu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Tsohuwar da Birai Suka Raineta, Tace a Wurinsu Take Samun Natsuwa

Maganin Gargajiya
Yadda Yan Nigeria Ke Ta'ammali Da Maganunuwan Da Zasu Illartar Dasu Basu Sani Ba Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A Nigeria masu tallen maganunuwan gargajiya na amfani da amsa-kuwa ko kuma kusa da wajen taron mutane a lokacin ibada ko kuma wani biki.

Maganunuwan na zuwa ne a mazubi, ko kuma kunshe cikin leda a nau'in ruwa-ruwa, ko kuma gari ko kuma mai da za'a iya shafawa.

Matsayar Majalissar Dikin Duniya Kan Maganin Gargajiya

Maganunuwan gargajiya kamar yadda masu su suke fada suna samo su ne daga ganyeyyeki, itacuwa, saiwa, didigen jikin bishiya da sauransu.

Majalissar dinkin duniya WHO, bata fitar da wani tsayayyen tsari da ake amfani da shi ba, musamman ma game da maganunuwan gargajiya.

Ko lokacin annobar cutar korona, kasar Madagascar ta samar da maganin cutar da tace yana yiwa yan kasarta aiki, amma majalissar dinkin duniyan tai watsi da batun tare da kin karbarsa.

Kara karanta wannan

Jihohi 10 Mafi Zaman Lafiya a Najeriya: Cikakken Jerinsu

Gargadin Masana Game da Maganin Gargajiya

Amfani da maganin gargajiya kan cutar tare da illatarwa a gargadin da masana lafiya sukai.

Babbar matsala da msana suke fada shine yadda ake hada maganunun da suke siyarwa da kuma wurin hada su.

Wani masanin lafiya Prof. Tanimola Akande, yace akwai damuwa mutuka ace magani daya na maganin cututuka da dama, gasakiya wannan abun dubawa ne inji masanin.

Magani Daya: Amma Yana Magance Cuttuka Da Yawa

Yawan cin masu sai da magununuwan gargajiya na ikirarin cewa maganinsu ba iya maganin cuta daya yake yi ba.

Wasu na ganin wani yanayi da mutum yake ciki shine yasa yake jin kaman wata cuta ke damunsa, kmar yadda masu maganin gargajiyan ke ikirari.

Misali, idan mutum na ciwon baya ko gababobinsa na ciwo, masu maganin na alakanqanta hakan da sunan sanyi ne ya dameshi.

Baya ga wannan ilolin kuma akwai maganunuwan da ake bayarwa a gargajiyance da suke kara kuzari ga mata ko maza, wanda sune ma suka fi karbuwa a tsakanin al'umma. n

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: