Dan Shekaru 19 Ya Yi Taron Godiya Ga Allah a Kauyensa Bayan Ya Kera Motar G-Wagon
- Goody Chukwudi Nwa Eze, wani hakizikin matashi dan Najeriya ya shirya taron godiya ga Allah kan motar da ya kera
- Matashin mai shekaru 19 ya shafe tsawon shekaru uku yana kera wata mota mai siffar G-Wagon
- Ya ce bai koyi yadda ake kera mota a koina ba amma ya taba kera adaidaita sahu da wata mai sifar Lexus
Wani matashi dan Najeriya mai suna Goody Chukwudi Nwa Eze ya sha jinjina a soshiyal midiya kan kerawa kansa motar G-Wagon da ya yi.
Matashin mai shekaru 19 ya dauki sabuwar motar tasa zuwa wajen taron godiya a ranar sabuwar shekara a mahaifarsa ta Ikpamodo.
Matashin wanda yake haifaffen Enugu wanda ya kammala makarantar sakandare ya bayyana cewa ya dauke shi tsawon shekaru uku kafin ya kammala kera motar.
Goody ya bayyana cewa shi ya koyawa kansa kuma a baya ya kera adaidaita sahu da wata mota mai kama da Lexus. Ya hasko cikin motar mai kyau da gaban motar wanda ke bukatar karin aiki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jama'a sun jinjinawa matashin wanda ya fito daga Umi Agbo, Ikapmodo, Enugu-Eziie da karamar hukumar Igbo-Eze ta arewa, jihar Enugu.
Jama'a sun yi martani
Johnpaul Obiora ya ce:
"Taron godiya kan wani dalili, maimakon neman taimako sun tafi taron godiya. Su yi hankali fa.
"Ba dukannin yan kauyen ke jin dadin wannan abun ba."
Shadrach Akinkugbe ya ce:
"Babu ko mutum daya daga cikin yan siyasan Najeriya da zai taikawa wannan yaron abun da ke gabansu shine babban zabe da yadda sakamakon zabrn zai kasance duk rashawa ne."
Chieme Martha ya ce:
"Dan Allah ku ceci rayuwarsa ta hanyar fitar da shi daga kauyen. Kafin su tuna wannan yaron. Na lullubeka da jinin Yesu Almasihu."
Matashi ya kera 'motar kara' mai aiki da injin, bidiyon ya ba da mamaki
A wani lamari makamancin wannan, wani matashi ya kera hadaddiyar 'motar kara' da ke aiki da inji.
Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan sun ci karo da bidiyon motar a kafofin soshiyal midiya.
Mutane sun zagaye mutumin cike da mamaki yayin da suke kallon yadda yake sarrafa motar tasa wanda ya kera da katakai cike da kwarewa.
Asali: Legit.ng