Matsaloli 7 da Kwana da Garwashi a Daki Kan Iya Jawowa Mutum, Sai a Kula
- An ce lafiya uwar jiki, amma a nemawa jiki lafiya wasu ke tsoma kawunansu cikin wata matsalar ta lafiya
- Kunna gawarshi a kwana dashi ba sabon abu bane, mutane sun dauki hakan a matsayin mafita ga matsalar sanyi
- Sai dai, masana kiwon lafiya sun ba da shawarin a guji kwana da garwashi a daki, hazan na da matsala ga dan Adam
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Yayin da sanyi ke ci gaba da busawa a duniya, mutane da yawa na amfani da garwashi wajen dumama daki don samun damar zama cikin tsanaki.
Sai dai, shin kunsan hakan na da illa ga lafiya? Masana sun yi tsokaci game da wannan lamari, sun kuma fadi mafita.
A wata hira da BBC Hausa ta yi da Dr. Hadiza Ashiru, batutuwa sun fito na illolin da ke tattare da kwana da garwashin wuta a daki.
Ta fadi illoli bakwai da ka iya samun mutumin da ke kwana da garwashi, karshe kuma ta ba da shawarin yadda za a samu sauki a wannan sanyin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Illoli 7 na kwana garwashi
Ga illolin da ta bayyana kamar haka:
1. Jawo Gobara
Sanya garwashi a daki a kwana dashi yana iya haifar da gobara da ka iya kaiwa ga asarar dukiya da ma rai.
2. Garwashi na dauke da guba
Kwana da garwashi na iya haifar da illa ta lafiya, domin duk da rashin warinsa, yana tartsatso da sinadarin carbon mono oxide; mai illa ga huhu.
3. Matsalar numfashi
Ga masu cututtuka irinsu Asma, kwana da garwashi zai iya tada cutar ko kuma ya kai ga kisa.
4. Toshe hanyoyin iska
Sannan, kwana da garwashi zai iya jawo shakewar hanyoyin iska da ka iya kaiwa ga mutuwa.
5. Cutar da fata
Kwana da garwashi a daki zai iya busar da fata, daga nan ya haifar da mutuwar wasu abubuwan da ke kanta.
6. Cutar mantuwa
Hayakin da garwashi ke fitarwa zai iya haifar da cutar da ke da alaka da mantuwa.
7. Matsalar kwakwalwa
Ga mutanen da suka fara tsufa, amfani da garwashi a kwana dashi a daki kan iya haifar da cutar da za ta iya taba kwakwalwa duk dai ta sanadiyyar hayakin da ke fita.
Meye mafita?
Da take bayyana abin da ya kamata mutane su yi, Dr Hadiza ta bayyana cewa, babu laifi mutum ya kunna garwashi, a bude tagogin daki domin hayakin ya fita, amma kuskure ne kwana dashi.
Duba da illolin da ke tattare da wannan garwashi, ta shawarci jama’a da su kauracewa yawan amfani dashi don kwana ana jin dumi a dakuna.
Hakazalika, ta ce mafi kyau shine amfani da rigar sanyi, hula, safa kda bargo mai kauri wajen kwanciya don yakar dukkan sanyi.
A makon nan ne aka tsinci gawarwakin ma'aurata a Kano saboda kwana da garwashi da suka yi a daki.
Asali: Legit.ng