Zamfara: ‘Yan Sanda Sun yi Nasarar Ceto Mutum 15 Daga Dajika Bayan Anyi Garkuwa Dasu
- Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta ceto mutane 15 da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba dasu kan titin Gusau zuwa Zaria
- Hakan ya biyo bayan sace fasinjoji a ranar Talata gami da tafiya dasu cikin daji da 'yan ta'addan suka yi matsayin wadanda aka yi garkuwa dasu
- Bayan samun bayanai game da mummunan labarin, rundunar ta hanzarta shirya tawagar ceto da tabbatar da tsaro zuwa yankin, inda suka yi musayar wuta da 'yan bindiga tare da nasarar ceto mutanen
Zamfara - Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta ceto mutane 15 da 'yan bindiga sukayi garkuwa dasu kan titin Gusau zuwa Zaria, jaridar Vanguard ta rahoto.
An yi garkuwa da wadanda lamarin ya auku dasu ranar Talata gami da yin awon gaba dasu cikin daji.
Yayin zantawa da manema labarai a Gusau, kakakin rundunar, Muhammad Shehu ya bayyana yadda daga lokacin da suka samu labarin, rundunar ta shirya tawagar ceto da tabbatar da tsaro zuwa yankin.
Premium Times ta rahoto cewa, Shehu ya ce, bayan musayar wuta mai karfi, hakan ya tilasta hatsabiban yada makamansu gami da ranta a na kare zuwa daji, tare da barin wadanda suka yi garkuwa dasu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"’Yan sandan dake tawagar sun hanzarta shiga cikin dajen, inda suka gano mutane 16 wadanda suka hada da mata bakwai, maza shida da yara biyu.
"An bincika lafiyar wadanda lamarin ya faru dasu, sannan sun gana da kwamishinan 'yan sanda don karin bayani game da rahotannin sirri.
"Ba tare da jinkiri ba, za a sadasu da iyalansu.”
- A cewar Shehu.
‘Yan Sanda sun halaka ‘dan bindiga, sun damke 6 da ake zargi a Zamfara
A wani labari na daban, jami’an ‘yan sanda ba jihar Zamfara sun tabbatar da halaka wani ‘dan bindiga a karon battar da suka yi.
Sun kara da samun nasarar damke wasu shida wadanda ake zarginsu da zama ‘yan bindiga.
Duk da miyagun sun amsa laifukabai, sun tabbatar da cewa suna daga cikin wadanda suka addabi jihohin Zamfara, Katsina, Kebbi da Niger.
Daga cikinsu akwai yaran Bello Turji, Halilu Kachalla da wani shugaban ‘yan bindiga da ya addabi yankin mai suna Malam Tukur.
Za a kammala bincike kafin gurfanar dasu.
Asali: Legit.ng