Abun Bakin Ciki: Hayaki Ya Turnuke Wasu Ma’aurata Har Lahira a Kano
- Wani magidanci mai suna Sulaiman Idris da amaryarsa, Maimuna Halliru, sun hadu da ajalinsu lokaci guda a jihar Kano
- Ma'auratan sun rasa ransu sakamakon hayakin garwashi da ya turnuke dakinsu suna tsaka da bacci
- Kamar yadda rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana, sun kunna garwashi domin dumama daki sakamakon sanyi da ake yi amma sai aka hadu da bacin rana
Kano - Wani mummunan al'amari ya riski al'ummar kauyen Kwa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano yayin da wasu ma'aurata, Sulaiman Idris mai shekaru 28 da matarsa Maimuna Halliru, mai shekaru 20 suka mutu.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an tsinci ma'auratan ne kwance babu rai a kan gadonsu na sunnah.
An tattaro cewa ma'auratan sun kunna garwashi domin dumama dakinsu sakamakon yanayi na sanyi da ake ciki kuma a haka ne hayaki ya turnuke su yayin da suke cikin bacci.
Rundunar yan sanda ta yi martani
Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna, ya ce kakar mijin ta lura da rashin jin motsi daga bangaren ma'auratan don haka ta fasa kofar dakinsu inda ta gansu kwance magashiyan a kan gadonsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
SP Haruna ya ce an kwashi ma'auratan zuwa asibitin Muratala Mohammed da ke Kano inda likita ya tabbatar da mutuwarsu, rahoton PM News.
A cewarsa:
"A ranar 3 ga watan Janairun 2023 da misalin 2100hrs, an samu wani rahoto daga kauyen Kwa, karamar hukumar Dawakin Tofa, jihar Kano cewa an lura wasu ma'aurata, Sulaiman Idris mai shekaru 28 da Maimuna Halliru mai shekaru 20 basu fito daga dakin aurensu ba tun a ranar 02/01/2023 da misalin 2300hrs. Da kakar mijin ta fasa kofar dakinsu, sai ta ga ma'auratan kwance a kan gadonsu basa motsi, da kaurin hayaki a dakinsu.
"Da samun rahoton, kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda, ya umurci wata tawaga karkashin jagorancin CSP Ahmed Hamza, DPO na yankin Dawakin Rofa da su isa wajen. An kwashi mutanen daga wajen sannan aka kai su asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano inda likita ya tabbatar da mutuwar ma'auratan.
"Da fara bincike, an gano cewa mamatan sun kunna garwashi don dumama dakinsu saboda sanyi, sannan suka rufe koina lamarin da ya sa hayaki ya turnuke koina yayin da suke bacci. Sai dai, ana ci gaba da bincike.
"Kwamishinan yan sanda, ya shawarci al'ummar jihar Kano kan bukatar yin taka-tsan-tsan yayin amfani da wuta da lantarki da daukar matakan kare kai a wannan lokaci na sanyi wanda ke da matukar hatsari na afkuwar gobara."
An gano asibitoci da shagunan magunguna 130 da likitocin bogi suka bude a Kano
A wani labarin kuma, wani kwamiti a karamar hukumar Tudun Wada a Kano, ya ce sun gano asibitoci da shagunan sayar da magunguna 130 da likitocin bogi suka bude kuma suke gudanar da aiki a jihar.
Asali: Legit.ng