An Yi Bata Kash Da ’Yan Bindiga a Kaduna, an Hallaka ’Yan Bindiga Hudu
- Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka wasu 'yan ta'addan da suka kai hare-hare wasu yankunan jihar Kaduna
- An hallaka 'yan bindiga hudu, an kwato makamai da kudade daga hannun 'yan bindigan da aka hallaka
- Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da samun nasara kan 'yan bindiga a yankuna daban-daban na kasar nan
Jihar Kaduna - Rundunar Operation Forest Sanity ta hallaka wasu ‘yan ta’adda hudu tare da kwato makamai da wasu kayayyakin aikata kaifi a jihar Kaduna.
Wannan na fitowa ne daga bakin Manjo Janar Musa Danmadami, daraktan yada labarai na gidan soja a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja, PM News ta ruwaito.
Danmadami ya bayyana cewa, jami’an tsaron sun dakile harin ‘yan bindiga a yankin Rafin Sarki a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a ranakun Lahadi da Litinin.

Kara karanta wannan
Shikenan: Daga karshe, an kashe shugaban 'yan bindigan da ya addabi mazauna jiharsu Buhari

Asali: UGC
Yadda aka hallaka 'yan bindigan tare da kwto makamai
Ya kuma kara da cewa, an fatattakin ‘yan bindiga tare da kashe biyu da kuma kwato makami AK-47.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kara da cewa, rundunar a ranar Talata ta yi kwanton bauna ga ‘yan bindiga kan wasu ‘yan bindiga a kauyen Rafin Taba, inda aka kashe ‘yan ta’adda biyu.
Ya ce jami’ai sun kwato bindigogi AK-47, alburusai, wayoyin hannu, adda, babura guda biyu da kudi N206,000.
Sanarwar ta ce:
"Babban ofishin rundunar sojoji ta yabawa dakarun Operation Forest Sanity kuma tana karfafawa jama'a gwiwa da su ba sojoji sahihan bayanan ‘yan ta’adda masu aikata laifuka.”
Asali: Legit.ng