Yadda Rabon Fada Ya Ja wa Matashin Bakano Rasa Hannunsa Daya
- Salisu Hussaini, wani wanda yayi kokarin kwantar da tarzoma ta hanyar tsaida rikicin da ya barke tsakanin makwabtansa biyu ya rasa hannunsa sanadin hakan
- Hakan ya biyo baya ne yayin da matashin mai shekaru 21 yayi kokarin raba fadan inda daya daga cikinsu yayi kokarin soka masa wuka a ciki, amma ya kare a hannunsa
- Telan wanda asibitin kashi na Dala ta yanke hannunsa da ya rube bayan kamuwa da cutar Tetanus, yayi kira ga hukumomi da su kwatar masa 'yancinsa
Kano - Matashi Salisu bai taba sanin sasanci da tsaida kwantar da tarzoma da shiga tsakanin makwabtansa 2 a Kano zaiyi sanadiyyar nakasarsa ba ta hanyar da bai yi tsammani ba.
Lamarin wanda ya auku a yankin Fagge cikin garin Kano yayi sanadiyyar da Husaini, matashin mai shekaru ashirin da daya yayi rashin hannunsa sakamakon soka masa wuka da wani hatsabibi, Abubakar Ayuba, da ake kira da Namama a yankin yayi.
"Nan Zan Kwana" Bidiyon Yadda Wani Mutumi Ya Gigita Diyarsa Yayin da Ya Shiga Dakin Tsohuwar Matarsa Ya Tube Kaya
City & Crime sun tattaro yadda rikici ya barke tsakanin Namama da matashi Abdullahi Muhammad, wanda ake kira da Alhaji Ozil, a karshen watan Maris, wanda yayi tsanani yayin da Salisu ya ga ya dace ya shiga lamarin don kwantar da rikicin amma daga karshe aka soka masa wuka wanda yayi sanadiyyar shigar cutar tatanos.
Yayin labarta yadda lamarin ya auku a gadon asibitinsa inda aka cire masa hannun, Hussaini yayi kira da babbar murya ga hukumomi da su samar masa 'yancinsa saboda bai taba tunanin rasa hannunsa ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewersa:
"A yayin da na gansu suna fada tare da barazanar kashe junansu, nace bari in shiga tsakani yadda za a samu lumana.
"Na tunkari Namama tunda na san irin rigimarsa gami da shawartarsa da ya kiyayi barazanar halaka mutane. Amma sai ya zaro wuka yayi yunkurin caka min a cikina, yayin da na kauce, ya soka min a hannu.
Kanwar Maza: Yadda Matashi Ya Kwanta a Bakin Gate Tare Da Garkame Shi Don Hana Maneman Auren Kanwarsa Shiga
"An kai ni asibiti inda suka bukaci mu zo da tare da 'dan sanda. Bayan an duba ciwon, hannuna bai warke ba.
"Sai muka tafi Asibitin Murtala Muhammad inda suka tura mu asibitin Malam Aminu AKTH daga baya zuwa nan Asibitin Kashi na Dala inda suka tabbatar da hannun ya lalace kuma dole a cire shi."
Rundunar 'yan sandan Kano ta tabbatar da aukuwar abun inda ta bayyana yadda suka kama wanda ya aikata mugun abun.
An sace kayan ango, an yi wuff da sadakin amarya
A wani labari na daban, wani ango a Kano ya shiga rudani bayan an sace kjayan da zai sa ya je daurin aurensa.
Ba a nan barawo ya tsaya da masa illa ba, ya sace sadakin da zai biya a daura auren yayin da aka je daurin auren.
Asali: Legit.ng