Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Tsohon Gwamnan Imo, Sun Kashe 'Yan Sanda

Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Tsohon Gwamnan Imo, Sun Kashe 'Yan Sanda

  • Tsagerun 'yan bindiga sun kai wani mummunan farmaki kan ayarin tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, ranar Litinin din nan
  • Bayanai sun nuna cewa harin wanda aka kulla da nufin tsohon gwamnan ya yi ajalin jami'an 'yan sanda hudu da ke ba shi tsaro
  • Wata majiya mai kusanci da Ohakim ta ce Direban da ke tukasa shi ya nuna kwarewa da basira wurin tsere wa maharan

Imo - Wasu miyagun 'yan bindiga da suka gudo daga wani wuri sun farwa ayarin tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, kuma sun halaka 'yan sanda hudu cikin masu ba shi tsaro.

Jaridar Punch ta rahoto cewa maharan sun farmaki Ayarin Ohakim ne a garin Oriagu, karamar hukumar Mbano ta jihar Imo da yammacin Litinin (yau).

Ikedi Ohakim.
Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Tsohon Gwamnan Imo, Sun Kashe 'Yan Sanda Hoto: punchng

Bayanai sun ce tsohon gwamna, wanda ya kubuta daga sharrin maharan, an ce bam ne ya tashi da Motar dake mara masa baya hakan ya yi ajalin dakarun 'yan sanda hudu.

Kara karanta wannan

Ashe babu dadi: Kasurgumin dan bindiga ya firgita, an rusa gidansa, an kashe yaransa 16

An ce Mista Ohakim na tare da 'ya'yansa guda biyu kuma suna kan hanyar komawa gida ne daga wata ziyara da suka je, ba zato 'yan bindigan suka far masu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya a kusa da tsohon gwamnan ta bayyana cewa sai da Direbansa ya yi dagaske ya nuna jajircewa sannan suka samu suka tsira daga mummunan harin.

Majiyar ta ce:

"Shi ne asalin abin harin amma Dirabansa ya nuna bajinta har ya samu nasara kan maharan saboda sun yi ta kokarin dakile su."
"Fushin rasa wanda suka shirya wa tuggun ya sa suka tare motar bayansa suka kone ta kurmus."

Jaridar The Nation ta tattaro cewa karin Dakarun tsaron da aka turo daga Owerri, babban birnin jihar Imo ne suka wa tsohon gwamnan rakiya har zuwa gida.

'Yan Bindiga Sun Banka Wuta a Gidan Mataimakin Shugaban Majalisa

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige Buhari da Tirka-Tirka 10 da Aka Yi a Majalisar Tarayya a Shekarar 2022

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kai wani kazamin hari garin Orsumoghu, karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra, sun tafka ta'adi

Rahotannin da muka tattara sun nuna cewa Maharan sun banka wuta a gidajen manyan mutane da ya haɗa da mataimakin kakakin majalisar dokokin jiha, Paschal Agbodike.

Baya ga haka, yan bindigan sun tafka ta'asa a harin, daga cikin gidajen da suka ƙona har da gidan shugaban al'ummar yankin, Nze Denis Muomaife.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262