Muhimman Abubuwa Guda Biyar Da Zasu Faru A wannan Shekarar 2023
- Shekarar 2023 ta kasance a zukatan mutane da dama, musamman ma ‘yan siyasa a Nigeria da kuma talakawan kasar
- Wasu abubuwa ne masu muhimmanci zasu faru a wannan shekarar wadda baza su sake faruwa ba a irin wannan yanayin
- Hatta shugaba Muhammadu Buhari wanda ya shugabanci Nigeria tsawon shekara bakwai da watannin zai bar mulki a wannan shekarar
Nigeria - Shekarar 2023 ta kasance wata shekara da ake yawan ambatonta da kuma muradin ganinta domin abubuwan da zasu kasance a cikinta.
Akwai wasu Muhimman abubuwa biyar da jaridar Legit.ng Hausa ta tattaro da zasu faru a wannan shekarar wanda yan Nigeria zasu gani ko kuma su ji.
1. Shugaba Buhari Zai Sauka Daga Mulki
Na da ga cikin abinda ‘yan Nigeria zasu gani shine yadda shugaba Muhammadu Buhari zai sauka daga karagar mulkin shugaban Nigeria, bayan shafe shekara takwas yana mulkar kasar.
Kusan karo hudu da shugaban ke neman darewa mulkin Nigeria tun daga shekarun 2003 har zuwa shekarar 2015 inda ya samu damar darewa bayan kada shugaban kasar lokacin Goodluck Jonathan.
A tsawon mulkin nasa an samu ci gaba mai yawa hadi da koma baya musamman ma a fannin tattalin arziki, noma da kiwo hadi da tsaro a fadin kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Zubin Majalissar Na Goma
A dai wannan shekarar ne dai za’a sauya majalissar kasa, ko kuma za’ai sabon zubi, inda za’a shiga majalissa ta goma, bayan karewar ta tara.
A lokacin da za’ai sabon zubin majalisasar ne ake zabar shugabannin majalissar da suka hada shugaban majalisar wakilai da ake kira da “Speaker” da kuma shugaban majalissar dattijai da ake kira da “Senate President”, baya ga manyan shugabannin majalissar kamar su mai rinjaye ko bulaliyar majalissa.
Wasu daga cikin sanatocin da kuma ‘yan majalissar zasu koma a karo na biyar ko hudu, ko uku ko biyu ko kuma wasu su shiga majalissar a karan farko.
3. Nigeria Zata Cika shekara 63 Da samun Yancin Kai
A dai wannan shekarar Nigeria zata cika shekara 63 da samun yancin kai, wanda ta samu daga hannun turawan mulkin mallaka a shekarar 1960 a farkon watan Oktoban shekarar.
Duk shekara Nigeria na murna cika shekara kaza da samun yancin kai, yayin da zata kirga riba ko akasarin ci gaban da ta samu.
Wani abu a bikin wannan shekarar da za’ai shine yadda ba shugaba Buhari bane zai jagoranci bikin da ya shafe kusan shekaru bakwai yanayi. Tun bikin cikar Nigeria shekara 56 Buharin ke jagorantar Bikin Inda yanzu kuma za’a samu sabon shugaban da zaiyi.
4. Wa’adin Shugabannin Hukumomin Gwamnatin Tarayya Zai Cika
Da yawa daga shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya kamar CBN, NITDA, Custom da dai sauransu zai cika bayan shafe wa’adin da kundin mulkin kasa ya basu na gudanar da hukumominsu.
Wasu hukumomin kundin tsarin mulki ya basu damar gabatar da shekaru hudu, yayin da wasu kuma kundin tsarin mulki ya basu damar gabatar da shekaru biyu ko uku.
5. Babban Zaben Nigeria
A watan biyu na wannan shekarar ‘yan Nigeria zasu zabi sabon shugaban kasar da zai musu shekara hudu akan karagar mulki tare da ‘yan majalissar wakilai dana dattijai da zasu jagoranci bangaran gudanar da doka a Nigeria.
A watan uku kuwa ‘yan Nigeria zasu zabi gwamnonin jihohinsu a karo na biyu ko karan farko tare da yan majalisar jihohin da zasi jagoranci gudanar da doka da oda a johihinsu.
Hukumar zaben Nigeria INEC, ce ta ke shirya zaben kuma ta ke gabatar da shi duk bayan shekarar hudu.
Asali: Legit.ng