Kyawawan Hotunan Ango da Amarya da Suka Bayyana Wurin Bikinsu a Napep

Kyawawan Hotunan Ango da Amarya da Suka Bayyana Wurin Bikinsu a Napep

  • Wani shugaban 'yan Napep ya angwance da masoyiyarsa a wani salon kwalisa da ado da suka sa mutane suka yi ta cece-kuce
  • Sabbin ma'auratan sun isa wajen shagalin bikin a jerin adaidaita sahu, wacce aka fi sani da Keke Napep
  • Sabon angon ya ce mutane da dama sun kasa yarda da yadda mutum mai matsayi irinsa zai tsaya hawa jerin adaidaita sahu a ranar bikinsa

Wasu ma'aurata masoyan juna 'yan Najeriya sun tada kura bayan sun bayyana a wajen shagalin bikinsu a jerin adaidaita sahu wacce kafi sani da Napep.

Ma’aurata a Napep
Kyawawan Hotunan Ango da Amarya da Suka Bayyana Wurin Bikinsu a Napep. Hoto daga Nniodo
Asali: Facebook

Angon mai suna Nniodo, 'dan shugaban masu adaidaita sahu na yankin, wanda ya taso daga Enugu, ta wallafa hotunansu a Facebook daga Majami'ar da aka daura auren, inda ya ce auren ya gabata ne ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Aboki Ya Dauka Bindigar Abokinsa 'Dan Sanda, yayi Masa Ruwan Alburusai, Ya Tsere da Bindigar

Nniodo ya bayyana cewa sun so bada mamaki ne ta hanyar amfani da adaidaita a matsayin abun hawan zuwa bikinsu.

A cewarsa, mutane sun kasa gasgata idonsu yayin da suka gansu a Keke Napep.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yayin da muka dosa wajen shagalin bikinmu, mun sha kallo, mutane sun kasa yarda cewa 'dan majalisa guda bai zai iya siyan Lamborghini ba sai dai hayar adaidaita sahu.”

- Kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Facebook.

Yayi addu’ar aurensu ya tabbata cikin farin ciki da kauna.

Tsokacin jama'a

Destiny ta ce:

"Wannan abu da ban sha'awa yake 'dan uwa! "Ina taya ku murna Ubangiji ya albarkaci aurenku Amen."

Victor Noble ya ce:

"Ji wani abu fa, dama ba a shirin kwaikwayo kadai ake irin wannan bikin ba...
"Ina taya ku murna kai, Ubangiji ya albarkaci gidan aurenku."

Kara karanta wannan

Jikinsa sumul: Bakaken yara sun gana da wani bature a karon farko, ya sha tambayoyi

Joseph Mary ta ce:

"Kai! Ina matukar taya ku murna 'dan uwa, da fatan wannan murmushin da farin ciki ya dawwama a gidan aurenku.
"Ina kara taya ku murna! "Rayuwa zallar nishadi ne a cikinta !

Amb Gabriel U Odi ya ce:

"Ina muku murna da sauran mutane.
"Ubangiji ya cigaba albarkatar gidan aurenku."

DWilliams Uchenna ya ce:

"Ina taya ka murna 'dan uwa. Ubangiji ya albarkaci gidan aurenku. Ban samu damar zuwa ba saboda rashin lafiyana. Na kwanta zazzabin mura da tari.

Budurwa na son tayi aure kafin ta mutu

A wani labari na daban, wata budurwa ta koka kan yadda mijin aure yayi mata wuyar samu.

Ta bayyana cewa tana fatan tayi aure kafin ta koma ga mahaliccinta baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng