A Ranar Aikin Karshe a Shekarar 2022, Buhari Ya Fitar da Sababbin Mukamai 9
- Muhammadu Buhari ya amince da nadin mukaman da aka yi a karkashin hukumomin FRSC da NLRC
- Darekta a ofishin SGF, Willie Bassey ya ce Dauda Biu da Lanre Gbajabiamila za su cigaba da rike kujerunsu
- A sanarwar, an ji Gwamnatin tarayya ta sabunta wa’adin Shugabar hukumar NAFDC da wasu Darektoci
Abuja - Mai girma Muhammadu Buhari ya amince da nadin wasu shugabannin hukumomi tare da sabunta wa’adin wasu da ke ofis a gwamnatin tarayya.
The Nation ta fahimci wannan ne a wata sanarwa da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya fitar ta ofishin Darektansa na yada labarai, Willie Bassey.
Sanarwar da aka fitar a yammacin Juma’a, 30 ga watan Disamba 2022, ta nuna Mista Dauda Ali Biu ya tabbata a matsayin Shugaban hukumar FRSC na Najeriya.
Wa’adin Dauda Ali Biu ya fara aiki ne tun daga ranar 23 ga watan Disamban nan, zai yi shekaru hudu a ofis, bayan nan za a iya kara masa wa’adi zuwa 2030.
Gbajabiamila zai zauna a NLRC
A jiyan ne aka samu labari gwamnatin Muhammadu Buhari ta sake nada Lanre Gbajabiamila a matsayin shugaban hukumar NLRC mai kula da harkar caca.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mista Lanre Gbajabiamila ya shiga wa’adinsa na karshe daga ranar 21 ga watan Nuwamban 2022. Hakan ya na nufin zuwa karshen 2026 zai bar hukumar.
Darektocin da aka nada
Baya ga shugabannin hukumomi, gwamnatin tarayya ta sake jaddada nadin wasu manyan Darektoci a hukumar RBDA mai kula da gabobin ruwa na kasa.
Leadership ta ce Darektocin da aka sake nadawa su ne Injiniya Bello Sani Gwarzo mai kula da tsare-tsare a hukuma da ke kula da ruwan Hadejia-Jama’are.
Injiniya Olatunji Babalola da Injiniya Olatunji Babalola za su cigaba da rike mukamansu har 2025.
A hukumar da ke kula da gabar ruwan Sokoto Rima, an sabunta wa’adin Mista Bashir Bala Zango a matsayin Darekta, shi ma zai karasa ragowar shekaru uku.
Akwai Mrs. Ononuju Mary Nwabunor wanda daga Disamban bana ta samu zama Darektan harkokin noma na hukumar kula da gabar ruwan Benin-Owena.
Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye
Kamar yadda aka samu rahoto a baya, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye za ta cigaba da jagorantar hukumar nan ta NAFDAC ta kasa zuwa Disamban 2027.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya wadanda aka zama murnar samun wannan dama, ya bukaci suyi amfani da kwarewarsu wajen sauki nauyinsu.
Babu karin albashi - Minista
A ranar Juma’ar nan ne kuma aka fahimci Gwamnatin Muhammadu Buhari ta bayyana cewa babu ma’aikacin da za ayi wa karin albashi a sabuwar shekara.
Chris Ngige ya fitar da wata sanarwa ta musamman ta bakin mai magana da yawun ma’aikatar kwadago, Olajide Oshundun kan lamarin albashi da ake ta yadawa.
Asali: Legit.ng