Murnar Ma’aikata ta Koma Ciki, Gwamnati Tace Ba Za a Kara Ko Sisi a Albashi ba
- Akasin labarin da yake yawo, gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta da niyyar kara albashin ma’aikata
- Ministan kwadago ya ce ba za ayi karin albashi ba, amma ana duba yiwuwar kara wasu alawus da ake biya
- Karin hasken ya fito ne ta bakin Kakakin Ministan Kwadago, Olajide Oshundun a yammacin Juma’ar nan
Abuja - Za a iya cewa Gwamnatin Tarayya ta lashe aman da tayi a kan maganar yin karin albashi ga ma’aikata da jami’an gwamnati a Najeriya.
Daily Trust ta rahoto Kakakin ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Mista Olajide Oshundun, yana yin karin haski a kan lamarin.
A ranar Juma’a, 30 ga watan Disamba 2022, Olajide Oshundun ya fitar da jawabi a jiya yana cewa gwamnati ba ta aiki kan albashin ma’aikatanta.
Mai magana da yawun bakin na Dr. Chris Ngige yake cewa wasu alawus ne kurum ake dubawa.
An yi amai a lashe kenan?
A baya an ji Ministan tarayyar ya nuna za a yi wa ma’aikatan gwamnatin tarayya karin albashi a shekarar badi, a dalilin hauhawar farashin kaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A karshe Aminiya ta rahoto ma’aikatar ta na cewa ba za a taba gundarin albashin ba, sai dai za a duba alawus da ake biyan wasu ma’aikatan gwamnati.
Dr. Chris Ngige ya ce kafin a fara karawa ma’aikata albashin da suke karba a kowane wata, dole sai an yi zama da wakilan kungiyoyin kwadago na kasa.
Gwamnati ta ce har zuwa yanzu ba a cin ma matsaya a kan wannan kari da ake tunanin za ayi ba. Karin nan zai shafi alawus din wasu daidaiku ne.
Za a gabatar da takardar duba alawus din ga Mai girma shugaba Muhammadu Buhari, idan ya amince da hakan, za a fara maganar yin karin kudin.
Magana ta je gaban PCS
Jawabin ya ce kwamitin shugaban kasa mai kula da harkar albashi na PCS ya karbi shawarar yi wa wasu ma’aikatun tarayya karin alawus ta ofishin SGF.
Ana sa ran wannan kari da ake niyyar yi ba tare da barazanar shiga yajin-aiki ba, zai taimaka wajen rage radadin da aka shiga a dalilin tashin farashin kaya.
Za a ƙara wa ma'aikata albashi - Ngige
A baya an rahoto Ministan kwadago da samar da aikin yi a Najeriya ya yi magana a kan karin albashi da albashin ‘Yan ASUU na watanni 8 da aka ki biyansu.
Chris Ngige ya nuna za a kara albashin ma'aikata a shekara mai zuwa, sannan ya kira 2022 da shekarar rigima da ‘yan kwadago ganin tataburzarsu da ASUU.
Asali: Legit.ng