Buhari Ya Sabunta Nadin Wani Mukamin Gwamnati Mai Muhimmanci

Buhari Ya Sabunta Nadin Wani Mukamin Gwamnati Mai Muhimmanci

  • A yayin da wa'adin shugaba Muhammadu Buhari ke daf da karewa, yana cigaba da yin nade-nade masu muhimmanci a hukumomin gwamnati
  • A baya-bayan nan, Shugaban kasar ya amince da sabunta nadin Farfesa Mojisola Adeyeye a matsayin direkta janar na NAFDAC
  • An rahoto cewa wa'adin Farfesa Adeyeye ya kare ne a ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba kafin shugaban kasar da ya fara nada ta a 2017 ya amince da sabunta nadinta

FCT Abuja - Wani rahoto da ke fitowa ya tabbatar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sabunta nadin Farfesa Mojisola Adeyeye a matsayin Direkta Janar na Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na kasa, NAFDAC.

Sayo Akintola, jami'in watsa labarai na NAFDAC ne ya tabbatar da sabunta nadin Farfesa Adeyeye, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Wata Fitacciyar Jami'a a Najeriya Ya Mutu Ba Zato Ba Tsammani

Shugaba Buhari
Buhari Ya Sabunta Nadin Wani Mukamin Gwamnati Mai Muhimmanci. Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sabunta nadin ta, kamar yadda Legit.ng ta tattaro zai fara aiki ne daga ranar Alhamis 1 ga watan Disamba bayan wa'adin da na farko wanda ya fara daga ranar 17 ga watan Nuwamban 2017 ya kare a ranar 3 ga watan Nuwamban 2022.

An kuma tattaro cewa gwamnatin tarayya ta nada Dr Monica Eimunjeze a matsayin mukadashin direkta janar na rikon kwarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164