Dattijon Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Bukaci Yan Najeriya Su Yi Watsi Da Kiran Sarkin Daura Kan Zaben 2023
- An bukaci yan Najeriya su yi watsi da kiraye-kirayen da wasu shugabanni a arewa ke yi na cewa mutane su zabi yan yankinsu yayin zabe
- Tanko Yakassai, ya ce manyan sarakuna masu daraja ta daya a arewa suna kokarin janyo hankalin mutane su zabi wadanda suke so a zaben 2023
- Dattijon kasan ya bukaci mutane su yi watsi da kiyayye da rabuwan kai da wasu shugabannin arewa ke koyarwa
Dattijon kasa, Tanko Yakassai, ya yi zargin cewa wasu manyan shugabannin arewa biyu na kokarin lalata hadin kan kasar.
Vanguard ta rahoto cewa Yakassai ya soki kiran da sarkin Daura, Alhaji Umar Farooq Umar ya yi na cewa yan arewa su zabi nasu a babban zaben 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A sanarwar da ya fitar mai dauke da sa hannunsa, Yakassai ya yi gargadin cewa yana da kyau kowa ya yi watsi da wannan yunkurin na mayar da kasar baya.
Ya bayyana cewa a baya, yan siyasa na amfani da wasu masu sarautun gargajiya don wanzar da mummunan kamfen din su, rahoton Independent.
A yayin da ya ke kira ga sarkin mai daraja ta daya kada ya bari yan siyasa suyi amfani da shi don wanzar da siyasar kabilanci, Yakassai ya yi zargin tsohon ministan noma, Sani Zangon Daura ya yi kira ga yan arewa su zabi nasu.
A cewar Yakassai, abin da Zango da sarkin suka aikata raba kan al'umma ne, kuma tsohon yayi ne da ba zai haifar da alheri ba.
Kalamansa:
"Na lura da yunkurin da wasu masu hannu a siyasa ke yi na farfado da tsohon al'adar da yan siyasa ke amfani da wasu sarakunan gargajiya wurin yin kamfen don muzanta wasu jam'iyyun a idon al'umma.
"Na ga yunkurin da wadannan manyan shugabannin arewa ke yi na lalata hadin kan Najeriya ta yadda kowa zai iya neman mukami bisa doka.
"Duk da yanzu na tsufa, akwai sauran kuzari tare da ni da zan iya yaki da irin wannan munanan al'adun a siyasan mai tsafta na yau."
2023: Twist as Powerful PDP Senator Asks Youths to Vote for Tinubu, Gives Strong Reason
2023: An Yi Mamaki Yayin Da Sanatan PDP Mai Tasiri Ya Bukaci Matasa Su Zabi Tinubu, Ya Bada Dalili
Zaben 2023: Yan garinsu Dogara sun juya masa baya, sun goyi bayan Tinubu
2023: Ta Kwabe Wa Dogara Yayin Da Shugabannin Kirista Da Yan Uwansa Suka Goyi Bayan Tikitin Musulmi-Musulmi Na Tinubu
Mutanen yankinsu Dogara sun juya masa baya, sun goyi bayan Tinubu na APC
A wani rahoton, daruruwan al'umma daga yankin da tsohon kakakin majalisar dokokin tarayya, Rt Hon Yakubu Dogara ya fito, sun fito sun bayyana goyon bayansu ga Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar APC.
Sun ce sun yanke shawarar goyon bayan dan takarar shugaban kasar na APC ne saboda irin ayyuka masu kyau da ya yi a jihar Legas lokacin yana gwamna.
Asali: Legit.ng