Gwamnatin Legas ta Shigar da Karar Zargin Kisan Kai Kan 'Dan Sanda da ya Halaka Lauya
1 - tsawon mintuna
Legas - Moyosore Onigbanjo, antoni janar na jihar Legas ya shigar da karar zargi daya kan kisan Drambi Vandi, 'dan sanda mai mukamin ASP kan kisan Bolanle Raheem.
An shigar da wannan zargin ne gaban wata kotun majistare dake zama a Yaba, Legas, a ranar Juma'a, jaridar TheCable ta rahoto.
An gurfanar da ASP Vandi a gaban mai shari'a Adeola Olatunbosun, wanda ya aike shi gidan yari.
"Cewa kai ASP Drambi Vandi a ranar 25 ga watan Disamban 2022 a wurin shatale-talen Ajah kan babbar hanyar Lekki-Epe dake Legas a cikin jihar ka kashe wata OmoBolanle Raheem ta hanyar harbe mamaciyar a kirji akasi da sashi na 223 na dokokin laifuka na jihar Legas, na 2015."
- takardar zargin ta bayyana.
Asali: Legit.ng