'Yan Sanda Sun Kama Yahoo Boys Da Suka Sace Abokin Aikinsu Don Ya Hana Su Kasonsu Cikin N22m Na Zamba
- Yan sanda sun cafke wasu da ake zargi da garkuwa da wani Haruna Usman a hukumar Obafemi Owode ta jihar Ogun
- Binciken farko da aka fara yi ya nuna cewa wadanda ake zargin yan yahoo ne kuma wanda suka sace abokin aikinsu ne
- Sun sace Usman ne saboda zarginsa da kin basu kasonsu cikin kudi N26m inda ya fada musu N2.2m kacal wanda suka damfara ya bashi
Jihar Ogun - Yan sanda a jihar Ogun sun kama wasu yan damfara ta intanet wato Yahoo Boys, kan zargin garkuwa da abokin aikinsu bisa 'rabon kudin zamba da suka samu', rahoton Daily Trust.
An kama wadanda ake zargin Agbe Simeon, Messiah Nicky (mace)’, Oladapo Dolapo da Yetunde Shonola (mace) a kauyen Orile Imo da ke karamar hukumar Obafemi Owode ta jihar Ogun.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kakakin yan sanda, Abimbola Oyeyemi, ya fada wa manema labarai a ranar Alhamis cewa an kama wadanda ake zargin ne a ranar Litinin bayan samun rahoton sace wani Haruna Usman a ofishin yan sanda da ke Owode Egba.
Ya ce an fada wa yan sandan cewa an sace Usman a ranar 22 ga watan Disamba kuma an tsare shi a wani wuri a Orile Imo, Vanguard ta rahoto.
Bayan samun bayanin, DPO na Owede Egba, SCP Popoola Olasunkanmi, ta tattara mutanensa sun tafi garin, inda suka kama hudu cikin wadanda ake zargi yayin da biyu suka tsere.
N2.2m ya basu cikin N26m, shi yasa suka yi garkuwa da shi - Yan sanda
Kakakin yan sandan ya ce binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin yan damfarar intaner ne da suka damfari wani kudinsa N26m.
A cewarsa, wanda abin ya faru da shi ya bawa abokansa N2.2m cikin N26m, yana ikirarin cewa wadanda suka damfara bai biya kudin baki daya ba.
Ya ce:
"Hakan ya fusata abokan aikinsa da suka yi masa dabara zuwa gidan boka a Orile Imo suka tsare shi tun ranar Alhamis 22 ga watan Disamban 2022, da barazanar za su kashe shi idan bai basu kasonsu na sauran kudin ba.
"Yayin da suke wurin, yan sandan sun samu bayani kuma suka garzaya suka kama wanda abin ya faru da shi da wadanda suka sace shi, wasu sun tsere."
Oyeyemi ya ambato cewa kwamishinan yan sanda Lanre Bankole, ya bada umurnin a mika wadanda ake zargin zuwa sashin binciken masu garkuwa da mutane na SCID don zurfafa bincike.
EFCC ta kama yan yahoo 41 da dukiyoyi masu yawa da suka mallaka
A wani rahoto, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama wasu da ake zargin yan damfarar yanar gizo ne wato yan yahoo guda 41.
Matasan sun kware wurin sace kudaden al'umma ta hanyar kutse cikin manhajojinsu na banki ko wayar salula ko kwamfuta.
Asali: Legit.ng