Gagrumar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Ogun Dake da Iyaka da Legas

Gagrumar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Ogun Dake da Iyaka da Legas

  • Gobara ta barke a wata kasuwa dake tsakanin iyakar Legas da Ogun, kasuwar Ajimula, wanda hakan yayi sanadin asarar kayayyaki da dukiyoyi da dama
  • Kasuwar ta fara ci ne misalin karfe 11:30 na daren Alhamis, yayin da hukumar kwana-kwana ta jihar Legas suka yi nasarar tsaida ta bayan isowarsu karfe 12:05 na dare
  • An fara kashe gobarar ne bayan isowar tawaga ta farko na hukumar kwana-kwana daga Ikeja kafin zuwan na Legas, duk da bata ci rai ba, an gano yadda rumfuna da gine-gine suka kone

Ogun - Wata kasuwa tsakanin iyakar Legas da Ogun, fitacciyar kasuwa ta Ajimula, ta kama da wuta wanda hakan ya lashe kayayyaki da dukiyoyi da dama, Daily Trust ta rahoto.

Gobara ce
Gagrumar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Ogun Dake da Iyaka da Legas. Hoto daga pumchng.com
Asali: UGC

An gano yadda gobarar ta barke a kasuwar dake gadar Kara cikin Isheri Olofin, wajen babban titin Legas zuwa Ibadan dake jihar Ogun misalin karfe 11:30 na daren Alhamis.

Kara karanta wannan

Kano: Masu Laifi 2,260 Suka Shiga Hannun Hisba, Ta Kwashe Almajirai 1,269 Tare da Tarwatsa Motocin Giya 25

Sai dai, hukumar kwana-kwana ta jihar Legas tayi nasarar kashe wutar.

Daraktar hukumar, Adeseye Magaret, a wata takarda ta ce 'yan kwana-kwana sun dakile gobarar daga yaduwa sauran sassan kasuwan, inda ta kara da cewa babu wanda gobarar ta ritsa da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Magaret:

"Hukumar kashe gabara da ceto ta jihar Legas ta samu kiran gaggawa misalin karfe 11:53 na daren Alhamis zuwa kasuwar duniya ta Ajimula wajen gadar Kara cikin Isheri Olofin dake jihar Ogun.
"An fara aikin kashe wutar ne misalin karfe 12:05 na dare bayan isowar 'yan kwana-kwana daga Alausa kafin sauran tawagar abokan aikinsu su iso saboda tsananin cin da wutar ke yi, wanda daga bisani aka kashe.
"Kasuwar ta kunshi rumfuna sama da kadada na fili. Gobarar ta lashe kayayyakin abinci da wadanda ba na ci ba irinsu jakunkunan leda, filastik, da sauran abubuwa irinsu babura.

Kara karanta wannan

Bayan Shakaru Takwas, Za'a Rataye Sagir Wada, Wanda Ya Yi Gunduwa-Gunduwa da Kishiyar Mamarsa a Kano

"Haka zalika, ta tsaida gobarar daga barin yaduwa cikin gine-ginen ba tare da ta ritsa da kowa ba.
"Har ila yau, ana yawan samun kiraye-kirayen gaggawa game da gobara duk da irin taka-tsantsan da hukumar ke shawartar jama'a a kai. An samu kiran gaggawa guda 22 a jiya, 28 ga watan Disamba bayan samun guda 24 a ranar kirsimeti."
"Ya kamata mu zama masu kula da irin wadannan abubuwan da ka iya jawo barkewar gobara."

- Shugabar ta shawarta.

Gobara ta tashi a kasuwar Singer

A wani labari na daban, gobara ta tashi a fitacciyar kasuwar Singer dake jihar Kano inda ta lashe kayan miliyoyin naira.

An gano cewa, jami'an hukumar kashe gobara sun hanzarta kai dauki gudun gobara tayi kamari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng