Kyakkayawar Budurwa ’Yar Arewa Ta Girgiza Intanet da Yadda Ta Kware a Buga Kwallon Kafa
- Wata kyakkyawar budurwa ta nuna kwarewarta a taka ledar tamola a cikin wani bidiyon da ya bazu a kafar TikTok
- Wani Aboubakar Siddiki ne ya yada bidiyon yadda budurwar ke buga kwallo cikin kwarewa lokacin tana daure da zane
- Mutane da yawa a kafar sun yi mamamki, akalla mutum 23k ne suka nuna sha’awarsu ga wannan kyakkyawan bidiyo
Wata kyakkyawar budurwa ta ja hankalin jama’a yayin da aka ga tana buga kwallon kafa cikin salo irin na kwararru.
A bidiyon da Aboubakar Siddiki ya yada a TikTok, an ga lokacin budurwar ke daure da zane kuma tana wasa da kwallo.
Duk da zanen da take daure dashi, hakan bai hanata buga kwallon cikin salo ba, ta buga kwallon yadda kwararru ke yi a filin wasa.
Tun daga farin daukar kwallon, da gani ka san ta saba bugawa, kuma ta samu horo mai kyau wajen yin wannan wasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yawan mutane na tsammanin kwallon ta fadi a lokacin da budurwar ke wasa da ita, amma sai ta ba da mamaki, ta zarce adadin da ake tsammani.
Wannan ya jawo martani a kafar sada zumunta, mutane da yawa sun bayyana abin da suka ji na mamaki game da budurwar.
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a
@Teeswagkd:
"Ya kamata wani ya fada min inda zan same ta.”
@user3172457851487:
"Wannan yarinyar daga wata kasa take haka.”
Salis:
"Kadarar Super Falcon kenan, na rantse.”
@Barde151:
"Ki ci gaba da aiki mai kyau.”
@11111:
"Nuna musu yadda Fulani ke da basira.”
@chukwunnaemeka365:
"Gaskiya tana basira.”
@user Fatimah:
"Tana bukatar goyon baya, ina kaunarki yarinya.”
@sulaimanharuna416:
"Kina da kokari.”
@chikekevin:
"Yanzu na gwada, daya na iya yi.”
@chukwunnaemeka365:
"Nima ina da daya ‘yar karama a nan.”
@Abdul Ice:
"A tawagarmu, kusan 90% ba za su iya wannan ba.”
Gwana ta gwanaye: Mai hijabi ta girgiza intanet yayin da ta nuna kwarewa a kwallon kafa
A wani labarin, wata budurwa sanye da hijabi ta ba da mamaki yayin da aga ganta tana taka leda cikin salon ban mamaki.
Jama'ar kafar sada zumunta sun shiga mamakin yadda budurwar ta samu kwarewa a buga wasan kwallo kamar maza.
Ba wannan ne karon farko da ake samun kwararrun 'yan mata da ke ba da mamaki a wasannin maza ba.
Asali: Legit.ng