Kotu Ta Hana Hukumar DSS Da EFCC Kama Emefiele Gwamnan CBN

Kotu Ta Hana Hukumar DSS Da EFCC Kama Emefiele Gwamnan CBN

  • Kotun tarayya da ke Abuja ta hana hukumar yan sanda farin kaya, DSS, kama gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele
  • Kotun karkahsin Mai shari'a M.A. Hassan ta ce hukumar ta DSS ba ta gabatar da hujojji ba ko wani abu na zahiri da ke alanka Emefiele da ta'addanci
  • Don haka kotun ta bada umurnin yan sandan farin kayan su kyalle Emefiele, su dena masa barazana, gayyatansa ko wani abu mai kama da hakan

FCT Abuja - Babban kotu da ke zamanta a Abuja ta bada umurni da ke hana Hukumar yan sandan farin kaya, DSS daga kama Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, The Cable ta rahoto.

Alkali M.A. Hassan ne ya bada umurnin a ranar Alhamis, ya kuma fadada umurnin ga sufeta janar na yan sanda, antoni janar na kasa, hukumar EFCC da CBN, da aka lissafa a matsayin wadanda aka yi kararsu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: NBA Ta Bukaci a Biya Iyalan Lauya Da Aka Kashe Diyyar N5b, Ta Ba Da Kwakkwaran Dalili 1

Gwamnan CBN
Kotu Ta Hana Hukumar DSS Da EFCC Kama Emefiele Gwamnan CBN. Hoto: The Cable
Asali: Getty Images

Yi wa Emefiele barazana ta saba doka

Da ya ke yanke hukunci a ranar Alhamis, baban kotun ta Abuja ta ce DSS bata gabatar da hujja ko wani abu na zahiri da zai nuna alaka da ta'addanci ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun ta kuma hana DSS daga cigaba da barazana, ko gayyaran, ko yin tambaya ko tsare gwamnan na CBN.

A baya, rahotanni sun zo cewa babban kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatan DSS na kama Emefiele kan zargi masu alaka da ta'addanci.

Hakan na zuwa ne yayin da ake hasashen cewa kama Emefiele na da alaka da siyasa, duba da tasirin da canja takardun naira da kayyade adadin kudaden da za a iya cirewa daga banki za su yi ka siyan kuri'u a zaben 2023.

Sauya takardun nairan da kayyade kudaden da za a iya cirewa ya janyo cece-kuce, yayin da majalisar tarayya a baya-bayan nan ta kame bakinta kan rashin bayyanar gwamnan na CBN a gabanta.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da motoci biyu suka yi karo, mutum 1 ya hallaka, yawa sun jikkata

Amma, cikin wata wasika da ya aike wa majalisar wakilan a ranar 21 ga watan Disamba, CBN ta ce Emefiele ya fita daga kasar don yin wasu ayyuka da duba lafiyarsa.

Yayin da ta bayyana gaban majalisar, Aisha Ahmad, mataimakiyar gwamnan CBN a bangaren tsarin daidaita kudade, ta ce ba don yan siyasa aka kawo sabbin sauye-sauyen ba.

Amma, CBN din ta sake nazari kan kayyade kudaden da za a iya cirewa, ta kara shi zuwa N500,000 ga daidaikun mutane da N5,000,000 ga kamfanoni.

Kotu ta yi fatali da bukatar kama Emefiele

A wani rahoton, wata babbar kotu a babban birnin Abuja ta yi fatali da bukatar hukumar DSS na neman izinin kama gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Kotun ta bakin mai shari'a John Tsoho ta ce abin da DSS ta nema bai kai a bata izinin kama gwamnan na CBN ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164