Yanzu Yanzu: NBA Ta Bukaci a Biya Iyalan Lauya Da Aka Kashe Diyyar N5b
- Tun farko kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA, ta fito ta yi Allah wadai da kisan wata lauya mace, Bolanle Raheem da wani jami'in dan sanda ya yi
- A wani ci gaba, kungiyar ta bayyana cewa za ta bukaci a biya iyalan marigayiyar diyya wanda ba zai gaza naira biliyan 5 ba
- A halin da ake ciki, an kashe lauyar wacce ke dauke da juna biyu yayin da suke kokarin juya motarsu a karkashin gadar Ajah, jihar Lagas
Wani rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta ce za ta nemi a biya akalla naira biliyan 5 a matsayin diyya ga iyalan lauyar Lagas, Omobolanle Raheem, wacce aka kashe.
Kungiyar ta kuma ce za ta bibiyi shari'ar ASP Drambi Vandi, wanda ya harbe da kashe Misis Raheem a jihar Lagas a ranar Kirsimeti.
NBA ta fadi dalili
Mamba na kungiyar NBA rshen Lagas kuma mai rajin kare hakkin dan adam, Ebun-Olu Adegboruwa (SAN), a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba, ya ce an nada shi domin ya jagoranci tawagar da za su sanya ido kan shari'ar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Misis Raheem, wacce ke dauke da juna biyu, tana a cikin motarta a hanyarta na komawa gida daga coci tare da iyalanta lokacin da aka harbe ta a yankin Ajah na jihar Lagas.
Adegboruwa ya ce:
"Kungiyar NBA reshen Lagas tare da hadin gwiwar shugaban NBA Misa Y.C. Mikyau, SAN, sun yanke shawarar kasancewa cikin masu hukunta dan sandan a kokarinsu na ganin an kwatowa iyalan marigayiyar hakkinsu cikin gaggawa."
NBA na neman a biya iyalan marigayiyar lauyar diyya
"Kungiyar NBA na kuma neman gwamnatin jihar Lagas, gwamnatin tarayya, rundunar yan sandan Najeriya da hukumar yan sanda su biya iyalan Misis Raheem diyya da hannun kwamitinta na kare hakkin dan adam."
Adegboruwa ya bukaci Gwamna Babajide Sanwo-Olu da ya bi tsarin da ya yi amfani da shi a lokacin kwamitin shari’a na EndSARS, rahoton TheNiche
"A biya iyalan Misis Raheem diyya ba tare da bata lokaci ba tunda a bayyane yake cewa jami’in dan sanda ne ya kawo karshen rayuwarta ba bisa ka’ida ba."
A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani dan sanda ya tsare lauyar tare da mijinta a ranar kirsimeti.
Sai dai kuma, yayin da mijin ke jiran motar gabansa ya motsa kafin ya faka, sai dan sandan ya harbi matar a kirjinta.
Asali: Legit.ng