Buhari Ya Kawata Kwamandan Dogaran Fadarsa Yayin da Ya Samu Karin Girma

Buhari Ya Kawata Kwamandan Dogaran Fadarsa Yayin da Ya Samu Karin Girma

  • Shugaba Muhammadu Buhari yayi jinjina ga shugaban dogaran fadarsa, Muhammad Usman da aka wa karin girma zuwa matakin Manjo-janar
  • Ya siffantashi a matsayin jami'in tsaro na musamman, wanda a koda yaushe shirye yake don hidimtamawa kasarsa cikin kaimi
  • A cewar Buhari, duk wadanda suka hidimta masasun san mutum ne wanda zai yi wahala ya yaba da kwazon mutum, amma bashi da wani dalilin kushe shi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya kambama kwamandan dogaran fadarsa da aka yi wa karin girma, Manjo-Janar Muhammad Usman, inda ya siffantasa a matsayin jami'in tsaro na daban wanda ke bautarwa kasa cikin kaimi.

Buhari da kwamandan dogaransa
Buhari Ya Kawata Kwamandan Dogaran Fadarsa Yayin da Ya Samu Karin Girma. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban kasar, a gaban Shugaban jami'an soji, Lt. Janar Faruk Yahaya da matar dogarin, Pharm (Dr) Rakiya Usman, ya kambama jami'in da ya samu karin girma zuwa matakin Manjo-janar.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: IGP ya fadi abin da ya kamata a yiwa dan sandan da ya kashe wata lauya mai ciki

Yayin jawabi jim kadan bayan bikin karin girman a fadar shugaban kasa, shugaban kasar yayi tuni game da irin hidimtamawa rundunar sojin da jami'in yayi, inda ya siffanta janar Usman a matsayin jami'i mai matukar sa'a duba da yadda ya kai kololuwa a matakin soji ba tare da sarewa ba.

Channels TV ta rahoto cewa, ya jinjinawa janar Usman bisa ga juriya, biyayya, hakuri da kokarinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ka na da matukar sa'ar samun isashshiyar lafiya da ikon gudanar da ayyukanka.
"Wadanda suka hidimtamin sun san ni mutum ne wanda ba a iyamawa. Amma ban taba samun wani dalili ko wata kafar kai kararka wajen shugaban sojin ko ministan tsaro ba.
"Babu wanda ya iya taba ni yayin da ka ke nan, na matukar yabawa da kwazonka."

- Shugaban kasan yace.

Shugaban kasar ya ce zai bada umarni kan aikin da Manjo-Janar zai yi a gaba, duba da yadda shima yake kokarin barin madafun iko, sannan kamar yadda ya saba fadi "zan koma wuri mai nisa daga Abuja."

Kara karanta wannan

Wadanda Ke Zagaye da Buhari Duk an Nada su Ba Don Cancanta ba, Jigon APC

Haka zalika, Shugaban kasa Buhari ya jinjinawa iyalan jami'in sojan bisa hakurinsu wajen jurewa da aikinsa mai matukar wahala da yake aiwatarwa ba tare da sarewa ba.

Usman yayi godiya

A jawabinsa, Manjo-Janar Usman yayi godiya ga shugaban kasar bisa karfafawarsa matuka ga dogaran fadarsa, inda ya kafa miaali da amincewa da samar da matocin yaki 400, wanda ya ce sun isa bada tsaro ga yankin aikinsa duk da babban birnin tarayya, jihar Nasarawa da yankunan jihar Neja.

Ya bayyana matukar farin cikinsa da karin girman da aka yi masa, inda ya ce hakan zai sa ya kara jajircewa wajen aiwatar da ayyukansa.

Karawa babban dogarin Aisha Buhari matsayi ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, karawa babban dogarin Aisha Buhari, Usman Shugaba, matsayi ya tayar da babbar kura.

An gano cewa, duk da akwai wadanda suka fara aiki tare fiye da matsayinsa, a halin yanzu yayi wuff ya wuce su a matsayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng