Kyakkyawar Budurwa Ta Fada Kogin Son Wani Boka, Bidiyonsu Ya Ja Hankali
- Wata kyakkyawar budurwa ta yi murnar kammala shekarar 2022 da samun masoyi bayan wahalar da ta sha a gidan aurenta na farko
- An gano matashiyar a wani kogi tare da wani boka bayan ta fada tarkon sonsa harma aure ya kullu tsakaninsu
- Yayin da take farin ciki da rayuwar da ta tsinci kanta a yanzu, matashiyar ta ce yanzu ta koma mahaifarta
Wata matashiya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta bayyana cewar ta fada tarkon son wani boka.
Ta bayyana cewa tun tana karamar yarinya take mafarkin rayuwa a kasar mahaifiyarta kuma hakan ya zama gaskiya da taimakon soyayya.
Matashiyar ta ce ta fara 2022 da rikicin gidan aure a Mexico amma ga shi zata kammala shekarar da burin zuciyarta.
Ta wallafa wani bidiyonta tare da bokan a wani kogi da kuma wasu bidiyoyin sharholiyarsu a TikTok.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Matashiyar ta yi farin ciki da komawa ga al'ada da salsalarta.
Bidiyonta na dauke da taken:
"Wato wannan ne dalilin da yasa Afrika ke ta kiran sunana tsawon shekaru da dama? Tun ina karamar yarinya nake mafarki kan ranar da zan yi rayuwa a kasar mahaifiyata. Dole na kasance a nan don riko ga yancina na yar kasa, al'ada da kambun sarauta ta! Na so wa kaina haka.
"Halin da kake ciki a yanzu ba shine makomarka na har abada ba. 2022 ya fara mun da rikicin cikin gida a Mexico sannan yana karewa cikin labarin soyayya da Ubangiji ne kawai zai iya samar da hakan a mahaifata. Whew! Allahuakbar!"
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
N van Lartey ta ce:
"A ina yake? Ina ta neman boka na hakika a accra."
Fedora The Goddd ta ce:
"Kai wannan ya hadu kuma ya yi kyau."
Kagi ta ce:
"Na aiko da sakon soyayya daga Afrika ta kudu."
dhee ta ce:
"Hadi daga Allah?"
joy ta ce:
"Ya yi kama da wannan dan wasan na kasar Kenya Lolani Kalu."
Matashiya mai tallan tuwo a Najeriya ta koma Turai tare da mijinta
A wani labarin, Allah ya tarbawa garin wata kyakkyawar matashiya yar Najeriya da ke sana'ar tuwo nono, inda ta keta hazo.
Matashiyar dai da mijinta sun yi balaguro inda suka koma Turai da zama.
Asali: Legit.ng