Majalisar Dattawa Ta Amince Da Bukatar Buhari Na Kara Kasafin Kuɗin 2022

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Bukatar Buhari Na Kara Kasafin Kuɗin 2022

  • Majalisar Dattawan Najeriya ta zartas da karin biliyan sama da N819bn a kasafin kuɗin 2022 dake gab da karewa
  • A makon da ya shige ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika da karin kasafin ga majalisun tarayya
  • Kudin dai zasu tafi ma'aikatu hudu ne da suka hada na Ma'aikatar noma, ruwa, FCT da ayyuka kuma za'a nemi bashi ne don aiwatar da karin

Abuja - Majalisar Dattawa ta Najeriya ta amince da kari ga kasafin kuɗin shekarar 2022 dake gab da karewa da zunzurutun kuɗi naira Biliyan N819.5bn.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya nemi majalisar ta amince da ƙarin kasafin, wanda a cewarsa za'a aiwatar da shi ta hanyar karɓo bashi.

Majalisar dattawa.
Majalisar Dattawa Ta Amince Da Bukatar Buhari Na Kara Kasafin Kuɗin 2022 Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Channels tv ta tattaro cewa gwamnati ta ware ƙarin kasafin kɗun domin magance matsalar ƙarancin abinci sakamakon ibtila'in ambaliyar ruwan da aka yi fama da ita a sassan ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan Raba Gari da Atiku, Gwamnonin PDP 5 Zasu Gana da Ɗan Takarar da Suke Shirin Goyon Baya a 2023

Haka zalika Biliyoyin Nairan dake kunshe a kundin ƙarin kasafin 2022 zasu tafi domin gyara Titunan da Ambaliyar ta lalata da kuma ɓangaren samar da ruwan sha.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnatin Buhari zata samar da kuɗin aiwatar da ƙarin kasafin kuɗin ne ta hanyar sake karbo bashi kuma zai kara yawan kasawar kasafin zuwa Tiriliyan N8.17tr.

Kwamitin kuɗi na majalisar dattawan Najeriya ne ya shawarci Sanatocin bisa jagorancin Sanata Ahmad Lawan da su zartas da bukatar karin kasafin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ma'aikatun da karin kasafin zai shafa

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa karin kasafin zai tafi ne zuwa ma'aikatar noma, ma'aikatar albarkatun ruwa, ma'aikatar birnin tarayya Abuja da ma'aikatar ayyuka da gidaje.

Jadawalin abinda ƙasafin ya kunsa ya nuna cewa ma'aikatar Noma zata samu Biliyan N69bn, Ma'aikatar Albarkatun ruwa biliyan N15.5bn, Ma'aikatar FCT biliyan N30bn sai kuma ma'aikatar ayyuka biliyan N704bn.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Jirgin Rundunar Sojin Sama Ya Yi Hatsari, An Rasa Rayuka

A wani labarin kuma Kun ji cewa Kudin Da Aka Sace Karkashin Buhari Idan Aka Rabawa Yan Najeriya Kowa Zai Samu N700,000

Kwamishina a hukumar jin daɗin yan sandan Najeriya ta yi ikirarin cewa kuɗin da aka yi sama da faɗi da su a gwamnatin APC sun zarce tunani.

Naja'atu Muhammed ta ce da za'a dawo da kuɗin a raba wa yan Najeriya kowane mutum ɗayazai iya tashi da sama da N700,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262