Kungiyar ASUU ta Bayyana Wanda Ya Yaudare su Aka Janye Yajin-Aiki a Jami’o’i

Kungiyar ASUU ta Bayyana Wanda Ya Yaudare su Aka Janye Yajin-Aiki a Jami’o’i

  • Kungiyar ASUU ta zargi shugaban majalisar wakilan tarayya da yi mata shigo-shigo babu-zurfi
  • Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce Femi Gbajabiamila ya jawo suka janye yajin-aikin watanni 8
  • Shugaban ASUU ya ce malaman jami’o’i sun hakura sun koma aji ne da tunanin za a cika masu alkawari

Abuja - Kungiyar malaman jami’o’i watau ASUU ta zargi shugaban majalisar wakilan tarayyan Najeriya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da yaudarar ta.

Jaridar Tribune ta rahoto kungiyar ASUU ta na cewa yaudarar da Femi Gbajabiamila ya yi mata, ya jawo aka janye yajin-aikin tsawon watanni takwas.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce shugaban majalisar ya nuna masu gwamnati za ta biya su albashin da suke bi.

Emmanuel Osodeke ya ce shugaban majalisar ya yi masu alkawari a rubuce cewa da zarar sun janye yajin-aikinsu, albashinsu na dyk watannin za su fito.

Kara karanta wannan

Yan Daba Sun Kona Gidan Shugaban Jam’iyyar APC a Wata Jahar Kudu

Kamar da gaske Inji Osodeke

Da aka yi hira da shi a ranar Talata, 27 ga watan Disamba 2022, Farfesa Osodeke a Tribune, shugaban ASUU ya ce sun yi maraba da sa bakin majalisa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban kungiyar malaman jami’ar ya yi wannan fashin baki ne da aka jefa masa tambaya a game da halin da ASUU ta ke ciki da gwamnatin tarayya.

Shugaban majalisa
Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila Hoto: @SpeakerGbaja
Asali: Twitter

...Ashe duk bula ce - ASUU

Kungiyar ta nuna duk da sa bakin da shugaban majalisar ya yi, ba a iya biya masu bukatunsu ba.

Nairaland ta rahoto Emmanuel Osodeke ya na cewa da farko duk Duniya ta yabawa irin kokarin Rt. Hon. Gbajabiamila, ashe duk shigo-shigo babu zurfi ce.

Farfesan ya ce daga cikin sabanin da suka samu da gwamnatin Muhammadu Buhari shi ne ayi amfani da UTAS wajen biyan malaman jami’a albashinsu.

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure: Kudin da Aka Sace Ya Fi Karfin N70tr ko N80tr, Na Nuna Inda Aka Boye Su

“Har yau ga mu nan, babu abin da aka yi a kan alkawuran da aka yi mana, shiyasa shugaban majalisa bai fadi wani abin kirki ba, akalla a kan batutuwan, ba a yin maganar alkawuran da aka dauka."

- Emmanuel Osodeke

Alfarmar dalibai da iyaye aka ci

A hirar da aka yi da shi, Osodeke ya ce sun koma aji ne saboda iyaye da daliban Najeriya, sannan ya soki hukuncin da kotu tayi gaggawar zartarwa a kan su.

ASUU ta yi Allah-wadai da halin da harkar ilmi ya shiga a karkashin mulkin Muhammadu Buhari, ya ce zai yi kyau gwamnati mai zuwa ta sa dokar ta-baci.

Za a kama shugaban APC

A wani umarnin gaggawa, an ji labari Mai girma David Umahi ya ce ‘yan sanda su yi ram da Shugaban APC da ‘dan takaran majalisa a dalilin kashe-kashe.

Kwanan nan Gwamnatin David Umahi ta ci jam’iyyar APC mai mulki da PDP, APGA da kuma LP tarar N5m saboda laifin sabawa dokar yin kamfe a Ebonyi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: Hadimin Gwamnan Jam'iyyar APC Ya Mutu a Hatsarin Mota

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng