Tsoho Ya Roki Malamin Addini Kan Ya Aura Masa Mata Ta Biyar, Bidiyon Ya Haddasa Cece-kuce
- Wani dattijo wanda ya je bauta a cocin Fasto Ezekiel Odero ya bar malamin addinin cikin mamaki bayan ya gabatar da bukatarsa
- Tsohon ya bukaci Ezekiel da ya taimaka masa da matar aure, yana mai cewa mata biyu da ya fara aura sun bar shi sannan ya sake auren wasu biyu amma suka mutu
- Mutumin wanda ke zaune a yanzu babu aure ya ce yana neman dattijuwa yar shekaru 52 zuwa 59 kuma wacce ta daina haihuwa don so yake ya hole a karshen rayuwarsa
Kenya - Wani dattijo mutumin kasar Kenya ya yiwa cocin Fasto Ezekiel Odero da Mavueni, Kilifi tsinke sannan ya bukaci malamin addinin da ya yi masa addu'an samun matar aure.
Fasto Ezekiel ya cika da mamaki bayan mutumin ya roke shi mata
Mutumin wanda kansa ke cike da furfura ya ba Ezekiel labarin yadda ya auri mata hudu a baya amma a yanzu ya saura babu mace.
Budurwa Mai Tallan Tuwo a Najeriya Ta tsallake, Ta Tare Da Mijinta a Turai, Sun Bar Jama'a Baki Bude
Dattijon ya bayyana cewa matasan biyu da ya fara aura sun rabu da shi sannan ya sake auren wasu biyu amma su dukka suka mutu kuma yanzo yana neman wacce za su yi rayuwa tare.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Faston wanda ke auren Fasto Sarah ya tambaye shi : "Shin kana son sabuwar mata?"
Sai dattijon ya amsa da:
"Eh, ina son sabuwar mata amma bana son wacce za ta haihu. Ina son dattijuwa tsakanin shekaru 52 zuwa 59. Wacce ba za ta zo da tarin bukatu ba don yarana su iya daukar dawainiyarmu mu biyu."
Ya kara da cewar:
"Ba na son samun karin 'ya'ya saboda bani da sauran fili da zan basu kuma ba zan iya daukar dawainiyar makarantarsu ba. Kawai ina son matar da zan iya more rayuwa tare da ita cikin farin ciki."
Bukatar da mutumin ya gabatar ya bar Ezekiel da mabiyansa cikin mamaki.
Da dama sun cika da mamakin bukatar da mutumin ya gabatar, inda wasu ke cewa zuwa neman shawara da addu'a a wajen Ezekiel kuskure ne don baya goyon bayan auren mata da yawa da na masu tazarar shekaru.
Magidanci mai yara 102 na fama da rayuwa
A halin yanzu, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wani dattijo mai shekaru 67, Musa Hasahya, wanda ke zama a Lusaka, Uganda, ya bayyana cewa yanzu baya so ya sake haihuwa.
Manomin ya yanke shawarar ne bayan ya haifi yara 102 da jikoki 568 daga mata 12.
Asali: Legit.ng