Sarkin Musulmi: Dalilin Da Yasa Muke Kiran El-Rufai Babban Mutum a Makaranta Duk Da Karancin Ruwansa
- Mai martaba sarkin Musulmi ya jinjinawa Gwamna Nasir El-Rufai kan yadda ya kawata garin Kaduna
- Sultan na Sakkwato ya ce a lokacin da suke makarantar sakandare suna yiwa gwamnan na jihar Kaduna lakabi da babban mutum duk da kankantar jikinsa
- Basaraken ya ce sunan ya samo asali ne saboda yadda yake da manyan ra'ayoyi da suka fi girmansa
Kaduna - Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya tuna yadda suke kira Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da 'babban mutum' a lokacin da suke makarantar sakandare a Kwalejin Barewa da ke Zaria.
Sarkin Musulmi ya fadi hakan ne a yayin da yake jawabi wajen kaddamar da babban ofishin gidauniyar zaman lafiya da ci gaba na Sultan a ranar Talata, 27 ga watan Disamba, a Kaduna, Daily Trust ta rahoto.
Ba Lallai Rashin Tsaro Ya Kare Ba a Najeriya Nan Da Shekaru 30, Inji Fitaccen Manazarci a Jami'ar BUK
Within Nigeria ta nakalto Sultan yana cewa:
"Lokacin da Nasiru yake kwalejin Barewa, yana kasa dani a aji, kuma muna kiransa da babban mutum. Za ku ga cewa karamin jiki ne da shi amma muna kiransa babban mutum, saboda muna kallon shi a matsayin mutum mai manyan ra'ayoyi, wanda tunaninsa sun fi jikinsa girma; saboda haka kuma da ya zama ministan birnin tarayya, mun ha abun da ya yi a Abuja, ya yi amfani da manyan motocin rusau wajen ruguza gine-gine da dama.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Lokacin da ya sake zuwa Kaduna, ya aikata irin haka sannan ina so na ce, tarihi zai fadi alkhairi kan Nasiru saboda abun da ya yi wa Kaduna. Ya yi abubuwa da dama, amma abu guda da zan dauka a ciki shine kawata garin Kaduna saboda ba za ka iya sanin ina kake ba idan kana tuki a hanya.
"Wannan abu guda ne da nake ganin tarihi za ta yi adalci gare shi saboda wannan. Akwai sauran abubuwa da dama da ya yi, mai kyau da mara kyau, amma a rayuwa ba za ka taba zama laifi ba muddin rayuwarka. A kodayaushe muna rokon Allah madaukakin sarki ya sa zunubin da za mu aikata ya gaza alkhairinmu don mu yan adam ne."
A wani labarin, gwamnan Jihar Kaduna ya mikawa Alhaji Abdullahi Daniya sandar girma a matsayin sarkin Jere na 11.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka yi bikin mika sandar girman a filin wasa na Jere a ranar cike da matakan tsaro.
Asali: Legit.ng