Zaman Da Na Yi a Gidan Kaso Yasa Na Zama Mai Kan-kan Da Kai, Tsohon Gwamna Jolly Nyame
- Jolly Nyame, tsohon gwamnan jihar Taraba ya magantu a kan yadda tsarin shari'ar kasar nan ke aiki
- Tsohon gwamnan ya ce ya lura tsarin shari'ar Najeriya na aiki ne daidai da matsayin mutum a kasar
- Nyame wanda ya yi zama a gidan kaso ya yi martani ne a ranar bikin cikarsa shekaru 67, watanni bayan yi masa afuwa
Tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame, wanda ya shafe tsawon shekaru uku a gidan gyara hali bayan an yanke masa hukunci kan karkatar da kudaden jama'a har naira biliyan 1.64 ya bayyana halin da ya shiga yayin da yake gidan yari.
Da yake bayyana wasu daga cikin abubuwan da ya koya a zaman da yayi a gidan gyara hali, Nyame ya ce tsarin shari'ar Najeriya na aiki ne daidai da matsayin mutum, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yiwa Nyame afuwa saboda yawan shekaru da kuma rashin lafiya.
An yanke masa hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari a shekarar 2018 kan karkatar da kudaden gwamnati.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga bisani, an rage masa yawan shekarun da zai yi zuwa 12 a 2020 bayan hukuncin da kotun koli ta yanke, inda ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara kan lamarin.
An saki Nyame daga gidan gyara hali na Kuje, Abuja a watan Agusta.
Shari'a iri biyu ne a Najeriya na masu gata da marasa galihu, Nyame
Da yake zantawa da manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, a ranar bikin cikarsa shekaru 67 a duniya, Nyame ya ce ya koyi darasi da dama a gidan yari.
Ya ce:
"Na koyi abubuwa da dama a zaman da nayi a gidan yari kuma na gane cewa a kasar nan, akwai shari'a iri biyu: daya na yan kasa masu gata sannan dayan na yan Najeriya marasa gata. Fatana shine cewa bayan 2023, abubuwa za su inganta."
Ya kuma bayyana cewa har abada zai ci gaba da godiya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan afuwar da ya yi masa.
Nyame ya kara da cewa:
"A matsayina na wanda ya amfana daga karamcin shugaba Buhari, ba zan taba bijire ma shugaban kasar ko bashi kunya ba a duk abun da zan aikata."
Na ji a jikina ba zan shekara 14 a kurkuku ba
Jaridar Punch ta kuma rahoto cewa Nyame ya ce a lokacin da alkali ya yanke masa hukuncin shekaru 14 a gidan yari, ya ji a jikinsa cewa ba zai kai tsawon wannan lokaci ba.
Ya kuma ce ya yi farin ciki matuka lokacin da aka yi masa afkuwa don ya san cewa abun da ya same shi mukaddari ne daga Allah.
A wani labari na daban, yan baranda sun farmaki gidan shugaban jam'iyyar APC a jihar Ebonyi inda suka cinnama gidan wuta.
Mummunan al'amarin ya afku ne a daren ranar Litinin, 26 ga watan Disamba kamar yadda majiya ta bayyana.
Asali: Legit.ng