Borno: Mayakan Boko Haram Sun Halaka Makiyaya 17 a Sabon Hari

Borno: Mayakan Boko Haram Sun Halaka Makiyaya 17 a Sabon Hari

  • Wasu da ake zargin mayakan ta'addancin Boko Haram ne sun halaka rayukan makiyaya 17 a kauyen Airamne dake Mafa a jihar Borno
  • An gano cewa, arangama aka yi a tsakanin makiyayan da 'yan ta'addan kuma suka halaka su tare da kwashe shanunsu
  • Shugaban 'yan sa kan yankin, Babakura Kolo ya tabbatar da cewa mayakan sun fi karfin makiyayan, kuma artabu aka sha kafin su halaka su

Borno - Wasu da ake zargin mayakan ta'addanci na Boko haram ne sun halaka makiyaya 17 tare da sace shanunsu bayan mummunar arangama da suka yi a Borno, 'yan sa kai suka sanar da AFP a ranar Litinin.

Mayakan ta'addancin a ranar Asabar sun kai farmaki kan makiyayan dake tsare shanunsu a wani filin kiwo dake kauyen Airamne dake yankin Mafa, 'yan sa kan suka sanar.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Farmaki Garuruwan Kebbi, Sun Kashe Mutum Biyu Tare Da Garkuwa Da Wasu 10

Taswirar Borno
Borno: Mayakan Boko Haram Sun Halaka Makiyaya 17 a Sabon Hari. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

"Makiyaya 17 aka halaka a fadan kuma aka yi kuma aka yi awon gaba da shanunsu."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

- Shugaban 'yan sa kai Babakura Kolo yace.

"Makiyayan sun nemi hana 'yan ta'addan aiwatar da mugun nufinsu amma an fi su da makamai da yawa, inda mayakan suka yi amfani da makamai."

- Kolo yace.

Channels TV ta rahoto cewa, wani 'dan sa kai mai suna Ibrahim Liman ya kara jaddada cewa mutane 17 ne suka rasa rayukansu.

Yace mayakan ta'addancin sun kaddamar da farmakin daga sansanoninsu dake kusa da dajin Gajiganna, inda suka koma bayan matsanta musu da sojojin Najeriya da ISWAP suka yi a dajin Sambisa.

Rabuwar kan ISWAP da Boko Haram

ISWAP sun rabe daga Boko Haram a shekarar 2016 kuma sun kai ga matakin mamaye kungiyar ta'addanci dake yankin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Kwana 1 da kashe tarin mutane, 'yan bindiga sun sake kai mummunan hari a Arewa

Ta kwace iyakoki dake karkashin Boko Haram karkashin shugabancin Abubakar Shekau wanda aka kashe a watan Mayun shekarar da ta gabata yayin arangama da ISWAP.

Boko Haram da ISWAP suna cigaba da kai farmaki kan fararen hula, ballantana manoma da makiyaya, wadanda suka zargi da kai bayanansu ga sojojin Najeriya da 'yan sa kan yankin.

Amma makiyayan da suke biyan haraji ga 'yan ta'addan ana barinsu su yi kiwon shanunsu hankali kwance a wuraren da 'yan tada kayar bayan ke mulka.

Kaduna: 'Yan Sanda Sun Damke Dillalin Makamai

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna tayi nasarar cafke wani Bilyaminu Saidu kan zargi zama dillalin makamai.

An kama shi ne a garin Basawa dake Zaria inda aka gan shi yana kokarin kaiwa tawagar miyagu makaman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng