Matasa da Malaman Addinin Islama Sun Halarci Zaman Cocin Ranar Kirsimeti a Kaduna

Matasa da Malaman Addinin Islama Sun Halarci Zaman Cocin Ranar Kirsimeti a Kaduna

  • Matasa da malaman addinin Islama da dama sun samu halartar kirsimetin wannan shekarar gami da mika kyautukansu don karfafa alakar dake tsakanin Kirista da Musulmi
  • Hakan yazo ne ana tsaka da tsadar rayuwa, rashin tsaro, talauci da tsadar kayan abinci, rashin aikin yi da karancin zaman lafiya a fadin kasar
  • Kamar Fasto Yohanna Buru ya bayyana, sama da musulmai 1000 sun halarci bikin kirsimetin wannan shekarar gami da mika kyautukansu ga kiristoci

Kaduna - Matasan Musulmai da manyan malaman addinin Musulunci sun halarci taron bikin Kirsimetin wannan shekarar gami da mika kyautukansu don karfafa alakar da ke tsakanin Kirista da Musulmi a arewacin kasar nan.

Musulmi
Matasa da Malaman Addinin Islama Sun Halarci Zaman Cocin Ranar Kirsimeti a Kaduna. Hoto daga pulse.ng
Asali: UGC

Kamar yadda babban fasto, Fasto Yohanna Buru ya bayyana, a kowacce shekara daruruwan Musulmai daga jihohin arewa guda 19 suna zuwa taya zagayowar ranar haihuwar Yesu a majami'arsa, don inganta zaman lafiya da hadin kai.

Kara karanta wannan

Matsanancin Halin Talaucin da za ka bar mu Ciki ya fi Wanda ka Tarar da mu, Kukah ga Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Farfesa Isah Mshelgaru, shi ne shugaban kungiyar musulman da suka taya murnar Kirsimeti da Kiristoci a majami'ar EYN dake Samarun Zaria, wadanda suka gabatarwa Rabaran Tijjani Chindo kyautuka yayin bikin kirsimeti a Zaria ranar Lahadi.

Buru ya ce kungiyoyin musulmai da dama, duk da 'yan kungiyar Tijjaniyya, 'yan Shi'a karkashin addinin musulunci na Najeriya da sauran musulmai ahlussunna sun taya su murna don tabbatar da zaman lafiya da hakuri da addini.

Kungiyoyin musulmai suma sun gabatar da kyautuka ga Majami'ar don nuna alamar zaman lafiya, soyayya da fahimta juna.

"Sun zo da kyautuka da dama da jinjina wanda suka raba ga Kiristoci don karfafa alakar dake tsakanin Kirista da Musulmi."

Jaridar Guardian ta rahoto cewa, Malamin addinin kiristan ya ce bikin kirsimetin wannan shekarar yazo ne ana tsaka da tsadar rayuwa, rashin tsaro da tsadar kayan abinci, talauci, da rashin aikin yi dake addabar zaman lafiya da daidaito a cikin kasar.

Kara karanta wannan

Ba Mu Tsayar Da Tinubu Don Zama Shugaban Kasa a 2023 Ba, Kungiyar Inyamuran Arewa

Buru ya kara da cewa a shekarar da ta gabata, sama da usulmai 1000 sun halarci bikin kirsimetin sannan sun zo da kyautuka da dama don mikawa ga Kiristoci maza don karfafa hakuri tsakanin addinan biyu.

Haka zalika, Buru yayi kira ga malaman Musulunci da na Kirista da su dage wajen addu'a ba tare da kakkautawa ba da fatan za a yi zaben 2023 lafiya.

Jaridar Pulse ta rahoto cewa, yayi kira ga 'yan Najeriya da su yi addu'a ga rundunar sojin Najeriya da hukumomi tsaro don cin galaba bisa kalubalen rashin tsaro dake addabar zaman lafiya a fadin kasar.

A zantawar da Legit.ng Hausa tayi da wani matashi mai suna Yahaya da ya halarci cocin a Samaru, ya sanar da cewa an yi mus karbar hannu bibbiyu tare da gwangwaje su da abinci da nama.

"A gaskiya sun yi mana tarbar arziki kuma mun ji dadi. Mun ci abinci, nama da ruwan lemo kuma hakan gaskiya ya kara dankon alaka a tsakaninmu."

- Yahaya yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng