‘Yan Sanda Sun Cafke Mutum 4 Yayin Dakile Yunkurin Yi wa Banki Fashi da Makami

‘Yan Sanda Sun Cafke Mutum 4 Yayin Dakile Yunkurin Yi wa Banki Fashi da Makami

  • Rundunar 'yan sandan jihar Cross Rivers tayi nasarar dakile harin bankin da wasu da ake zargin 'yan fashi da makami ne suka kai wani banki
  • An yi nasarar cafke hudu daga cikin tara da ake zargin sun kai harin wani tsohon bankin babban birnin Calabar
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar ya lashi takobin zakulo biyar daga cikin maharan bankin ba tare da jinkiri ba

Cross River - Rundunar 'yan sanda jihar Cross River ta bayyana yadda ta dakile wani fashi da makami a daya daga cikin tsoffin bankunan Calabar, babban birnin jihar.

Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, Sule Balarabe, kwamishinan 'yan sandan jihar, ya ce rundunar tayi ram da wasu hudu da ake zargin suna da hannu a dakilallen harin, jaridar TheCable ta rahoto.

'Yan Sanda
‘Yan Sanda Sun Cafke Mutum 4 Yayin Dakile Yunkurin Yi wa Banki Fashi da Makami. Hoto daga Thecable.ng
Asali: UGC

Vanguard ta rahoto, ya ce wadanda ake zargin sun hada da Joshua Samuel mai shekaru 22; Innocent mai shekaru 20; Samuel Okon mai shekaru 28; da Muhammad Salisu mai shekaru 29.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dan Bindiga a Kaduna, Sun Kwato Bindigogin AK47 Guda 4

A cewarsa, wadanda ake zarginsu da fashin biyar daga ciki sun tsere.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Bayan samun bayanan sirri, supal na EPZ ya hada tawaga gami da yin dirar mikiya bankin, tare da damko hudu daga cikin tara da ake zargin."

- Kamar yadda NAN ta yanko jawabinsa.

"Hudun da aka kama sune wadanda suke aikata ayyukan ta'addancin, su kuma biyar daga ciki suna waje suna gadi tare da jiran harbi.
"Yayin tuhumarsu, wadanda ake zargin sun bayyana burinsu na fashin da shirin sanar da sauran tawagar 'yan fashin lokacin da ya kamata su yi harbi tare ko lokacin da ya kamata su yi sata a bankin."

- Yace.

Balarabe ya bada tabbacin cewa za a kamo 'yan fashin da suka tsere ba da jimawa ba. Sannan ya ja kunnen hatsabiban da ke cin karensu ba babbaka a cikin anguwa ko dai su bi doka ko kuma a kawo karshensu.

Kara karanta wannan

Wa ya kaiku: An gurfanar da 'yan APC da PDP 14 a Borno bisa aikata wani babban laifi

"Dukkan kwamandojin tawagar, DPO a shirye suke don magance ayyukan ta'addanci a kowanne yankin jihar, ta hanyar amfani da dabarbarun sanin makamar aiki."

- A cewarsa.

'Yan bindiga sun kai hari bankuna 3 a Kogi

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kai hari bankuna uku a lokaci daya a jihar Kogi.

Lamarin ya faru ne a watan Satumba inda 'yan fashin suka kwashi makuden kudade a bas bas da babura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng