Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dan Fashi Da Makami a Kaduna, Sun Kwato Makamai
- Yan sanda sun kama wani dan bindiga dauke da bindigogin AK47 da alburusai a yankin Kwarkwaron Manu da ke Zaria, jihar Kaduna
- Wanda ake zargin na a hanyarsa ta kaiwa abokan ta'asarsa makaman ne lokacin da jami'an tsaron suka yi ram da shi
- Sai dai wani abokin tafiyarsa da suke kan babur tare ya tsere kuma an bazama bincike don gano inda suke
Kaduna - Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani kasurgumin dan fashi da siyar da makamai inda suka kwato bindigogin AK47 guda hudu da alburusai 344 da babur dinsa.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Kaduna, Muhammad Jalige, ne ya tabbatar da kamun dan bindigar a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 25 ga watan Disamba, Vanguard ta rahoto.
Yadda al'amarin ya faru
Jalige ya ce jajircewar da jami'an rundunar ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya yayin bukukuwa ya fara haifar da 'ya'ya masu idanu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi bayanin cewa:
"A ranar 23 ga watan Disamba da misalin karfe 17:30, jami'an rundunar da ke Tudun Wada Zaria, yayin gudanar da wani fatrol a Kwarkwaron Manu, yankin Bawa da ke garin Zaria, sun cafke wasu mutum biyu da babura marasa rijista dauke da jakunkuna da aka nade.
"Da aka tsayar da su don bincike, fasinjan babur din ya yi tsalle sannan ya tsere, lamarin da ya karfafa zargin jami'an tsaron.
"An gaggauta binciken babur din da matukinsa wanda ya bayyana sunansa a matsayin Bilyaminu Saidu mai shekaru 33 daga kauyen Shuwaki da ke karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina, lamarin da ya kai ga kama shi.
"Kayayyakin da aka samu daga wajensa sun hada da bindigogin AK47 guda hudu, alburusai 344, wayoyin tarho da layu."
Jalige ya ce wanda aka kaman na nan a tsare kuma binciken farko ya nuna cewa shi da abokin tafiyarsa da ya tsere suna kan hanyar kaiwa abokan ta'asarsu muggan makaman ne, rahoton New Telegraph.
Ya kuma bayyana cewa kwamishinan yan sandan jihar Kaduna, Mista Yekini Ayoku, ya yi umurnin zurfafa bincike domin gano tushe da kuma inda za a kai makaman tare da kama abokan huldar wanda ake zargin.
Yan Hisbah sun kama matasa 19 da ke shirin auren jinsi daya a Kano
A wani labari na daban, jami'an hukumar Hisbah sun damke wasu matasa 19 yayin da suke taro da kokarin kulla auratayya tsakanin wasu samari biyu.
Asali: Legit.ng