Barkwancin da Ake Na Kira Na ‘Jubril Na Sudan’ Ba Abin Dariya Bane, Inji Shugaba Buhari

Barkwancin da Ake Na Kira Na ‘Jubril Na Sudan’ Ba Abin Dariya Bane, Inji Shugaba Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bacin ransa game da yadda wasu 'yan Najeriya ke kiransa da 'Jubril na Sudan'
  • Buhari ya ce hakan ba abin dariya bane, kuma bai kamata ake yayata abin da babu gaskiya a ciki ba
  • A 2018 ne aka kitsa wata manakisa, aka ce Buhari ya mutu an sauya shi da wani mutumun kasar Sudan mai suna Jubril

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai jin dadin yadda ake barkwanci a kansa ta hanyar kiransa da 'Jurbil na Sudan'.

A cewar Buhari wannan fade da mutane ke yi ba abin dariya bane, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Buhari ya bayyana hakan ne a daren Juma'a 23 ga watan Disamba, yayin bikin karrada shugaba mai kishin kasa da iyalansa suka shirya a bikin cikarsa shekaru 80.

Kara karanta wannan

Ta gudu ta barni: Dan acaba mai yawo da jariri a cikin riga ya fadi tarihinsa mai ban tausayi

Ba abin dariya bane a kira ni da 'Jubril na Sudan'
Barkwancin da Ake Na Kira Na ‘Jubril Na Sudan’ Ba Abin Dariya Bane, Shugaba Inji Buhari | Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Yadda aka fara barkwanci kan Buhari

Idan baki manta ba, a shekarar 2018 an yada wata jita-jitan cewa, shugaba Buhari ya mutu, kuma an dauko wani mai suna 'Jubril na Sudan' domin ya zama kininsa don ci gaba da shugabantar kasar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan jita-jita ya yadu a Najeriya ne bayan da shugaban ya dawo gida Najeriya, inda shafe kwanaki 103 a kasar Burtaniya yana jinyar wani rashin lafiya.

Buhari ya fada a wani bidiyon da aka dauka cewa, makiya ne ke yada wannan jita-jitan don kawai cimma wani burinsu.

Da aka tambaye shi ko hakan ya ba shi dariya, shugaban ya ce sam ba haka bane, babu dadi, ba abin dariya bane kana hakan zai iya kawo cikas a cikin al'umma.

Ya kuma bayyana cewa, 'yan Najeriya sun iya kirkiro shirme kan abin da suka gaza fahimta kai tsaye, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Buhari Ya Bayyana Adadin Kujerun Da Jam'iyyar APC Za Ta Lashe

Ban damu da sunan ba, amma ba abin dariya bane, inji Buhari

Ya ce:

"Tabbas! Mutane sun ce ni wani ne daga Sudan. Ban damu da sunan ba. 'Yan Najeriya suna da munanan hanyoyin bayyana kansu."
"A'a. Ba abin dariya bane saboda wadanda suka kirkiri batun, kawai suna son nuna rashin girmamawa ne. Suna son kawar da hankali ne daga asalin abin da ake kai.
"Babban abin da ke gabanmu shine ababan more rayuwa, mu sanya mutane su san cewa suna bukatar aiki tukuru don su rayu da kyau. Kawai so suke so yi sharholiya ba tare da nemawa kansu girmamawa daga al'umma da sauransu ba."

Da yake martani game da maganar da aka fada tun 2018 a karon farko, Buhari ya ce duk da mutane suna masa fatan mutuwa, shi din dai shine, kuma lafiyarsa kalau.

A shekarar da ta gaba wani hadin Buhari ya bayyana gaskiyar jita-jitan da ake yadawa da kuma yadda hakan ke tasirantuwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Aiki ya jika: Bayan kowa ya yi ankon N150k, amarya ta fece, ango da abokansa sun girgiza

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.