Kwana Daya Dayan Yin Jana’azar Mutane da Yawa, ’Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari Kaduna
- Wasu 'yan bindiga sun sake kai mummunan hari a jihar Kaduna jim kadan bayan hallaka mutane da yawa a jihar
- An ce sun zo da manyan makamai, sun yi harbin kai mai uwa da wabi, amma jami'an tsaro suka lallasa 'yan ta'addan
- Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalolin 'yan bindiga, musamman a 'yan shekarun nan
Kaura, jihar Kaduna - Kwana guda bayan da aka yi jana’aizar tulin mutanen da aka kashe a Mallagum-Kagoro a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna, ‘yan bincika sun sake kai wani mummunan hari a daren Juma’a 24 ga watan Disamba.
Harin yazo kwanaki biyu kafin bikin Kirsimeti ya faru ne da tsakanin karfe 9:00 zuwa 9:45 na dare yayin da ‘yan bindigan suka yi yi ta harbe-harben kan mai uwa da wabi.
Wani mazaunin yankin da ya zanta da jaridar Daily Trust ya shaida cewa, ‘yan bindigan sun zo ne da manyan makamai, kuma suka yi harbi kan mazauna kauye.
Sai dai an yi nasarar dakile harin, domin kuwa, sojoji sun zo cikin gaggawa tare da fatattakar ‘yan ta’addan.
Sai dai, ya zuwa yanzu dai ba a sami cikakken bayani a hukumance ba daga hukumomin gwamnati.
Hakazalika, majiya ta kira kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, Muhammad Jalige, amma bai amsa waya ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda aka yi jana'izar mutane da yawa a Kaduna
Idan baku manta ba, rahoto ya bayyana yadda wasu 'yan bindiga suka hallaka mutane da yawa a jihar Kaduna, an yi jana'izar akalla mutane 37, inji rahoton Channels Tv.
Jaruruwan mutane ne suka taru a kauyukan Malagum da Sokwong na karamar hukumar Kaura don wannan jana'iza ta mutanen da aka hallaka.
A yayin jana'izar, mutane da yawa sun bayyana jimami da kuma kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki ta kuma raba su da hare-haren 'yan ta'adda.
Gwamnati ta kashe makudan kudade wajen habaka aikin 'yan sanda
A wani labarin kuma, gwamnatin Buhari ta bayyana adadin kudaden da ta kashe wajen gyara ofisoshin 'yan sanda da bariki a kasar nan.
Hakazalika, gwamnati ta bayyana kashe biliyoyi wajen inganta wuraren horo da samar da kayayyakin aiki masu inganci.
Asali: Legit.ng