'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Daliban Kwalejin Fasaha a Jihar Ondo

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Daliban Kwalejin Fasaha a Jihar Ondo

  • Wasu mutane ɗauke da bindigu sun yi garkuwa da ɗaliban kwalejin fasaha hudu suna hanyar zuwa gida a jihar Ondo
  • Bayanai sun nuna cewa ɗaliban, waɗan da ke karatu a kwalejin jihar Kogi, sun shiga hannun masu garkuwa ne a yankin Akoko, Ondo
  • Kwamandan rundunar 'yan sanda yace tuni dakaru suka mamaye dazukan titin da lamarin ya faru don ceto wadan da aka sace

Ondo - Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi awon gaba da ɗaliban kwalejin fasa hudu yayin da suke kan hanyar zuwa gida don halartar bikin al'ada a jihar Ondo.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an sace ɗaliban ne akalla su huɗu a kan Titin Akunno zuwa Ajuwa da ke yankin Akoko, a jihar Ondo, kudu maso yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Arewa, Sun Kashe Basarake

Harin garkuwa da mutane.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Daliban Kwalejin Fasaha a Jihar Ondo Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Bayanai sun nuna cewa ɗaliban su na karatu ne a kwalejin fasaha ta jihar Kogi, kuma maharan sun masu kwantan ɓauna suka tasa su ranar Jumu'a a yankin Akoko.

An ce Titin Ago Jinadu, Akoko inda lamarin ya faru da sanannen wurim aikata muggan laifuka ne musamman garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai bayan faruwar nan lamarin, mazauna jarin Ajuwa sun shiga tashin hankali da fargabar abinda ka iya zuwa ya dawo.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Yayin da aka nemi jin ta bakinsa, kwamandan runɗmdunar 'yan sandan yankin, ACP Muri Agboola, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Ya ce tuni jami'an 'yan sansa suka mamaye Dazukan da ke kan Titin Akunnu-Ajowa, yankin Akoko da nufin kubutar da ɗaliban da maharan suka sace.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Banka Wuta a Gidan Mataimakin Shugaban Majalisa, Sun Tafka Ɓarna

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoton ba'a sami zantawa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Ondo, Funmi Odunlami, kan lamarin ba.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kaiwa Ayarin Dakarun Yan Sanda Hari a jihar Kogi, An Rasa Rayuka

Wasu 'yan ta'adda sun mamayi dakrun 'yan sanda masu aikin Sintiri a jihar Kogi, sun kashe jami'ai guda biyu.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kogi, William Aya, yace lamarin ya faru ne a kan Titin Agbaja, Lokoja ranar Laraba 21 ga watan Disamba, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262