Gwamna El-rufai Ya Bada Sandan Sarauta Ga Sabon Sarki A Kaduna
- Malam Nasir Ahmed El-Rufa'i, gwamnan jihar Kaduna ya gabatar da sandan sarauta ga sabon sarkin Jere, Alhaji Abdullahi Daniya
- An yi bikin mika sandan sarautan ne a ranar Juma'a 23 ga watan Disambar shekarar 2022 a filin motsa jiki na Jere
- Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe, Janar Tukur Yusuf Buratai (mai murabus), jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin na daga cikin wadanda suka halarci bikin
Jihar Kaduna - Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa'i na Jihar Kaduna ya gabatar da sandan sarauta ga Alhaji Abdullahi Daniya a matsayin sarkin Jere na 11.
An yi bikin ne a filin wasanni na Jere a ranar Juma'a tare da matakan tsaro, Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin da ya ke rantsar da sarkin, Gwamna El-Rufa'i ya mika godiya ga mutanen Jere saboda gudunmawa da suka bada wurin samar da zaman lafiya a yankin.
Ya ce gwamnatinsa na yin iya kokarinta domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin mutanen jihar.
El-Rufai ya bukaci mutanen jihar su cigaba da bawa jami'an tsaro hadin kai a yayin da suke kokarin fatattakar bata gari daga jihar.
Ya kuma yi kira ga mutanen masarautan Jere su zama masu biyayya ga sabon sarkin.
Wasu manyan baki da suka halarci taron
Hajiya Hadiza Balarabe, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, mambobin kwamitin zartarwa na jihar Kaduna, jakadan Najeriya ga Jamhuriyar Benin, Janar Yusuf Tukur Buratai (mai murabus) na cikin manyan bakin da suka halarci bikin ba da sandan.
Gwamnan Jihar Kaduna ya ba da sandar sarauta ga sarkin Lere
A wani rahoton, gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i, ya mika sandan sarauta ga sabon sarkin Lere, Alhaji Sulaiman Umaru, a ranar Laraba 29 ga watan Disamba.
Malam Umaru, ya gaji kawunsa, marigayi Sarki Abubakar na II, wanda ya mutu a farkon shekarar 2021.
Malam El-Rufa'i ya bukaci sabon sarkin ya yi koyi da halayen magabacinsa marigayi Abubakar, yayin jawabin da ya yi wurin bikin mika sandan sarautan.
Gwamnan ya kuma yi wa mutanen garin Lere alkawarin nan bada dadewa ba zai kaddamar da sashin ilimin noma na Jami'ar Jihar Kaduna a Lere.
Asali: Legit.ng