An Kama Wani Mai Garkuwa Da Mutane Yana Karbar Kudin Fansa N3m Daga Iyayen Wanda Aka Sace A Jihar Arewa

An Kama Wani Mai Garkuwa Da Mutane Yana Karbar Kudin Fansa N3m Daga Iyayen Wanda Aka Sace A Jihar Arewa

  • Yan sanda sun kama wani da ake zargi da garkuwa da mutane a jihar Plateau yana kokarin karbar kudin fansa na Naira miliyan 3
  • Bayan kama wanda ake zargin, yan sandan sun yi nasarar ceto yaro dan shekara hudu, Nazifi, mazaunin Zam Zam a Jos
  • Kwamishinan yan sandan jihar Plateau, Bartholomew Onyeka, ya kuma ce jami'ansa sun kama wasu masu garkuwa takwas

Plateau - Jami'an yan sanda a jihar Plateau sun kama wani wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne yana kokarin karbar kudin fansa na N3m daga mahaifin wanda ya sace, rahoton The Punch.

Kwamishinan yan sandan jihar Benue, Bartholomew Onyeka, ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a yayin da ya ke yi wa yan jarida jawabin 'nasarorin' da rundunar ta samu a hedkwatar yan sanda da ke Jos.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Gwamnan PDP Ya Rushe Ciyamomi 17, Mataimaka da Kansilolin Jiharsa

Taswirar Plateau
An Kama Wani Mai Garkuwa Da Mutane Yana Karbar Kudin Fansa N3m Daga Iyayen Wanda Aka Sace A Jihar Arewa. Hoto: Plateau
Asali: UGC

Yadda yan sanda suka kamo mai garkuwa a Plateau

Onyeka ya ce a ranar 21 ga watan Disamban 2022 misalin ƙarfe 1.20 bayan samun sahihan bayanan sirri, yan sanda na Division A sun kama wani Ashiru Ibrahim dan shekara 22 mazaunin Angwan Rogo da ke zargi da garkuwa da wani dan shekara hudu Abubakar Nazifi mazaunin Zam-Zam Abuja Mata Rikkos a Jos ranar 19 ga watan Disamba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce bayan kama shi, wanda ake zargin ya bayyana bayanai masu amfani wadanda suka yi sanadin ceto wanda abin ya faru da shi daga maɓuyar masu garkuwa.

Bayan zurfafa bincike an yi nasarar gano wani abokin hada bakinsa, Bashir Saleh, mazaunin Rikkos a Jos wanda shine ya fara garkuwar.

Yan sandan sun ce ana zurfafa bincike sannan daga bisani za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Arewa, Sun Kashe Basarake

An kama wasu karin masu garkuwa su takwas

Kwamishinan yan sandan ya kuma ce jami'ansa sun kama wasu masu garkuwa da mutane takwas a wasu samamen a karamar hukumar Quaapan bayan sun sace mata biyu.

Daga karshe ya gargadi bata gari su tuba su dena laifukan da suke aikatawa musamman lokutan bukukuwa yana mai cewa ya umurci jami'ansa su kasance cikin shiri kafin, yayin da bayan bukukuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164